Hare-haren Legas shiryayyu ne, yunkurin durkusar da tattalin arziki ne - Gwamnonin Kudu

Hare-haren Legas shiryayyu ne, yunkurin durkusar da tattalin arziki ne - Gwamnonin Kudu

- Akwai wata boyayyar munakisa a kan cigaba da zanga-zangar EndSARS wacce aka dade ana shiryawa, cewar Gwamnan Ondo

- Gwamnan, wanda ya ari bakin gwamnonin kudu maso yamma ya ci musu albasa, ya ce anyi asarar dukiyoyin jihar Legas ne don karya tattalin arzikin yankin

- Ya fadi hakan ne bayan ya gama zagaye jihar Legas, inda ya ga yadda bata-gari suka lalata gine-gine da dukiyoyin gwamnati da na al'umma

Gwamnonin kudu maso yamma sun bayyana asarar dukiyoyin da aka yi a jihar Legas a matsayin yunkurin durkusar da tattalin arzikin yankin, The Cable ta wallafa.

Rotimi Akeredolu, gwamnan jihar Ondo, wanda ya ari bakin gwamnonin ya ci musu albasa, ya sanar da hakan bayan zagaye jihar Legas da yayi ranar Lahadi.

Hare-haren Legas shiryayyu ne, yunkurin durkusar da tattalin arziki ne - Gwamnonin Kudu
Hare-haren Legas shiryayyu ne, yunkurin durkusar da tattalin arziki ne - Gwamnonin Kudu. Hoto daga @TheCable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Tallafin Covid-19: An gane mahaifina ba shine matsalar Najeriya ba - Zahra Buhari

Kamar yadda kakakin gwamnan jihar Legas, Gboyega Akosile, ya sanar a wata takarda, wacce Akeredolu ya misalta Legas da filin daga, ya ce irin asarar dukiyar da aka yi na da ban tsoro.

Gwamnan ya ce akwai wata manufa da tasa aka yi zanga-zangar wacce ta zarce ta dakatar da SARS a kasar nan.

KU KARANTA: Umarnin IGP: 'Yan siyasa da 'yan kasuwa sun cigaba da yawo da 'yan sanda

"Hakika munji radadin yadda aka kona dukiyoyin gwamnati, ma'adanai, ofisoshin 'yan sanda, gine-ginen gwamnati da dukiyoyin jama'ar wannan yanki, duk da kokari da jajircewar jami'an tsaro.

"Wannan al'amarin yasa muka fara tunanin akwai wata manufar cigaba da zanga-zangar, wacce aka dade ana shiryawa kuma ana tanadi akai," cewar Akeredolu.

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana sabon salon biyan albashin jami'an 'yan sanda, inda ya umarci hukumar albashi ta kasa da tayi gaggawar amsar canjin.

Shugaba Buhari ya fadi hakanne a jawabin kai tsaye a ranar Alhamis da yamma.

Buhari yace, "Don tabbatar da jindadi da walwalar 'yan sanda, an umarci hukumar albashi da tayi gaggawar tabbatar da sabon tsarin albashin jami'an 'yan sandan. Ana duba a kan yadda za'a bullo wa albashin sauran jami'an tsaro."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel