Da duminsa: Matasa sun balle gidan Yakubu Dogara, jami'an tsaro sun bude musu wuta

Da duminsa: Matasa sun balle gidan Yakubu Dogara, jami'an tsaro sun bude musu wuta

- Fusatattun matasa a jihar Filato sun kutsa gidan tsohon kakakin majalisar wakilan Najeriya

- Matasan sun balle gidan Yakubu Dogara da ke kusa da asbitin koyarwa na jami'ar jihar Filato

- Jami'an tsaro sun yi harbi don tarwatsa matasan amma hakan bai samar da wata nasara ba

A ranar Lahadi, wasu bata-gari sun shiga tare da yashe gidan tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, da ke kusa da asibitin koyarwa na jami'ar jihar Filato.

Jaridar Punch ta gano cewa, 'yan daban sun take dokar kullen da gwamnatin jihar ta saka musu inda suke ta kusatwa gine-gine domin neman kayan tallafin korona.

An kai harin gidan Dogara da karfe 9 na safe, wata majiya da ta kasance ganau ba jiyau ba ta sanar da Jaridar Punch.

'Yan sanda da sauran jami'an tsaron da ke tabbatar da an bi dokar kullen sun yi harbi domin tarwatsa taron matasan amma hakan bai sa an samu nasara ba.

"Sun balle gidan tsohon kakakin majalisar wakilai inda suka kai wa kowa hari, har da kaninsa. Sun dinga diban komai da suka samu.

"Matasan sun kwashe adaidaita sahu, kayan dakuna, kayan wuta da sauransu," wani ganau ya sanar da The Punch.

Karin baynai na nan tafe...

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel