Jihar Filato: Ɓata gari sun ɓalle ɗakin ajiyar taki da kayan aikin gona, sun kwashe komai

Jihar Filato: Ɓata gari sun ɓalle ɗakin ajiyar taki da kayan aikin gona, sun kwashe komai

- Bata gari sun sake fasa wani dakin ajiyar kaya a Jos, sun sace muhimman kayayyaki

- Gwamna Lalong ya sanya dokar ta baci a ranar Asabar, 24 ga watan Oktoba, a jihar domin kawo karshen sace-sace

- Bata garin sun kai farmaki hukumar PADP a ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoba, sannan suka sace wasu kayan gona

Lamarin sace-sace na ci gaba da yaduwa a garin Jos, babbar birnin jihar Filato duk da sanya dokar ta baci na sa’o’i 24 da Gwamna Simon Lalong ya sanya a wasu kananan hukumomi biyu na jihar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wasu bata gari karkashin inuwar zanga-zangar EndSARS sun fasa wasu dakunan ajiyan kayayyaki a yankunan Bukuru da Jos da ke jihar.

Legit.ng ta tattaro cewa wasu bata gari sun sake fasa wani dakin ajiya a hukumar ci gaban noma na jihar Filato PADP.

Jihar Filato: Ɓata gari sun ɓalle ɗakin ajiyar taki da kayan aikin gona, sun kwashe komai
Jihar Filato: Ɓata gari sun ɓalle ɗakin ajiyar taki da kayan aikin gona, sun kwashe komai Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Sama da babura 350, firinji 400, janareto, injin nika aka sace a gidana - Sanata Folarin

A cewar rahoton, dakin ajiyan na da zaman ne a yankin Dogon Dutse da ke karamar hukumar Jos ta arewa a jihar.

Gwamnan ya sake sanya dokar ta baci a ranar Asabar, 24 ga watan Oktoba, domin daidaita barnar da bata gari suka yi yayinda suke kai hari wuraren ajiyan kayayyaki.

Jaridar ta bayyana cewa bata garin sun kai farmaki dakin ajiya a hukumar PADP a safiyar ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoba, sannan suka sace buhuhunan taki da kayan aikin gona da aka ajiye a dakin.

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Miyetti Allah ta bankaɗo wanda ke ɗaukar nauyin Zanga-zanga

An tattaro cewa jami’ an tsaro sun isa yankin domin tarwatsa bata garin.

An gano mutane dauke da buhuhunan taki da sauran kayayyakin gona a kansu daga dakin ajiyan, inda suka tafi wurare daban-daban.

A gefe guda, wasu matasa sun kwashi buhunan kayan abinci bayan balle kofofin ma'adanar kayan tallafin COVID-19 na gwamnatin jihar Filato dake Jos a ranar Asabar.

Mutane 5 sun rasa rayukansu a Taraba yayin damben kwaso wasu kudade da aka gano a ma'adanar jihar Taraba, da ke babban birnin jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel