Wawushe tallafin Covid-19: Mutum 11 sun rasa rayukansu

Wawushe tallafin Covid-19: Mutum 11 sun rasa rayukansu

- Matasa sun cigaba da gano ma'adanar kayan tallafin COVID-19 na jihohi daban-daban suna kwashesu

- A jihohi kamar Kaduna, Ekiti, Benin, Anambra, Cross River, Taraba da Filato, matasa sun kwashe kayan tallafin tas

- Ba a kayan abinci kadai suka tsaya ba, sun yi awon gaba da kujeru, katifu, kudade da sauransu, wanda hakan ya jawo rasa rayuka

Batagari sun cigaba da yadda suka ga dama da dukiyoyin gwamnati da na al'umma sakamakon barkewar rikicin zanga-zangar EndSARS, Daily Trust ta wallafa.

A jihar Benin, Anambra, Edo, Kaduna, Filato, Cross River da Ekiti, matasa sun yi ta shiga ma'adanai, inda aka ajiye kayan tallafin COVID-19, wadanda ya kamata a raba wa talakawa, suna awon gaba da su.

Manema labarai sun tattaro bayanai a kan yadda mutane 5 suka rasa rayukansu a jihar Edo, 5 a jihar Taraba da kuma wani mutum a Anambra, duk sakamakon kwasar kayan abincin.

Wasu matasa sun kwashi buhunan kayan abinci bayan balle kofofin ma'adanar kayan tallafin COVID-19 na gwamnatin jihar Filato dake Jos a ranar Asabar.

Mutane 5 sun rasa rayukansu a Taraba yayin damben kwaso wasu kudade da aka gano a ma'adanar jihar Taraba, da ke babban birnin jihar.

An ga dubbannin mutane, har da mata da yara, suna kwasar kayan abinci daga ma'adanar.

An samo bayanan yadda matasa suka gano buhuna 2 cike da 'yan dubu daidaya, a ma'adanar. Sai suka bar kwasar kayan abincin suka fada wa kudaden.

Wata mata cewa tayi, "Mun kwashi rabonmu. 'Yan siyasa ba su da tausayi, sun adana kayan abinci amma mutane na fama da bakar yunwa."

A Kaduna kuwa, matasa sun gano wani gida a Barnawa, karamar hukumar Kaduna ta kudu, da ba'asan mai shi ba, inda aka ga kayan tallafin COVID-19.

Matasan sun kwashe har kayan wuta, kujeru da sauran kayan amfani da aka gani a ma'adanar.

Bayan faruwar hakan ne, gwamnatin jihar Kaduna ta saka kullen awanni 24, kuma ta umarci a kama duk wanda aka kama ya saba dokarta.

KU KARANTA: ICPC ta gurfanar da dan majalisar tarayya a kan karbar cin hanci daga 'yan kwangila

Wawushe tallafin Covid-19: Mutum 11 sun rasa rayukansu
Wawushe tallafin Covid-19: Mutum 11 sun rasa rayukansu. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sabon tsarin albashin 'yan sanda na zuwa nan babu dadewa - Buhari

A wani labari na daban, kamar yadda jaridar ThisDay ta wallafa, an ji harbe-harbe tare da ganin mummunar wutar gobara ta tashi a gidan gyaran hali da ke Ikoyi a jihar Legas.

Hakan baya rasa alaka da rikicin tare da tarzomar da ta barke a jihar tun daga zanga-zangar EndSARS. Jami'an 'yan sanda da sojoji sun isa gidan gyaran hali da ke Ikoyi a kokarinsu na datse yunkurin balle gidan da aka yi.

Kamar yadda bidiyon ya bayyana, an ga hayaki na fitowa daga wasu sassan gidan yarin yayin da 'yan gidan ke gudu domin neman wurin zuwa.

An gano cewa, hukumomin gidan gyaran halin sun gaggauta sanar da 'yan sanda da sojoji domin daukar matakin da ya dace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel