Mutum 5 sun mutu yayin rabon kuɗin da suka tsinnta a ma'ajiyar kayan tallafin korona

Mutum 5 sun mutu yayin rabon kuɗin da suka tsinnta a ma'ajiyar kayan tallafin korona

- Wasu utane biyar sun rasa rayukansu yayin kokawar rabon kudi da suka tsinta a ma'ajiyar abinci a Taraba

- Dubban mutanen sun balle wani dajin ajiyar abinci na gwamnati ne don dibar abincin tallafin korona amma suka tsinci kudi a wasu jakkuna

- Hakan yasa da dama cikin dubban mutanen da suka tafi diban abincin suka koma kokawa wurin rabon kudaden

An ruwaito cewa mutum biyar sun rasu yayin da suka ƙoƙarin rabon wani adadin kudi da suka tsinta a maj'ajiyar abinci na gwamnati a Jalingo, jihar Taraba.

Daily Trust ta ruwaito cewa mutanen sun ɓalle wurin ajiyar abincin ne inda suka tsinta jakuna biyu ɗauke da kuɗi ƴab dubu-dubu kusa da sakatariyar Kungiyar Kirista ta Najeriya a Jalingo ranar Asabar.

Daga nan ne suka yi watsi da abincin suka fara kokowar yadda za su raba kuɗin da suka tsinta.

Mutum 5 sun mutu yayin rabon kuɗin da suka tsinnta a ma'ajiyar kayan tallafin korona
Mutum 5 sun mutu yayin rabon kuɗin da suka tsinnta a ma'ajiyar kayan tallafin korona. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Ana harbe harbe a kasuwar Abuja yayin da ƴan sanda suka hana fasa ma'ajiyar abinci

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa mutanen da abin ya faru da su sun mutu yayin da dubban mutane suka yi ƙoƙarin kokawar ganin suma an raba kuɗin tare da su.

An gano cewa duk da mutum 5 sun mutu yayin ƙoƙarin rabon kuɗin wasu jami'an tsaro suma sun shiga kokawar.

An gano cewar an ajiye kayan abincin a daƙin ajiyar tun watanni hudu da suka gabata.

Rahotanni sun ce mutane maza da mata sunyi ta ɗibar kayan abincin wasu ma da ababen hawa suka taho.

Wasu cikin masu ɗiban kayan da aka tattauna da su sun ce da kuɗin al'umma ne aka siya kayan abincin.

KU KARANTA: El-Zakzaky yana nan da ransa - IMN

Wata mata ta ce, "muna kwasar kayan mu, ƴan siyasar nan azzalumai ne don sun ɓoye abincin duk da sun san mutane na fama da yunwa."

Da aka tuntube shi, sakataren dindindin na hukumar bada agajin gaggawa na jihar Taraba, Danazumi Navulga ya ce ba zai yi tsokaci kan lamarin ba don ya yi murabus.

Hadimin gwamnan jihar kan watsa labarai, Mista Bala DanAbu shima ya ƙi cewa komai.

"Idan kuma ma'ajiyar kayan abincin kuma ka ga abinda ya faru sai ka rubuta rahoton ka," inji DanAbu.

A wani labarin, wasu da ake zargi ƴan daba ne a ranar Asabar sun kai hari gidan Sanata Teslim Folarin dan jamiyyar APC mai wakiltar Oyo Central da ke Ibadan sun sace kayan tallafi da kuɗin su ya kai N200m.

Folarin ya tabbatar da faruwar mummunan lamarin yayin wani shirin gidan rediyo a ranar Asabar a Ibadan kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel