Matasan sun yi cincirindo a Jos domin diban kayan tallafin Korona (Bidiyoyi)

Matasan sun yi cincirindo a Jos domin diban kayan tallafin Korona (Bidiyoyi)

- Satan kayan tallafin Korona ya zama ruwan dare a jihohin Najeriya

- Matasa a jihar Plateau sun shiga kwasan nasu rabon tun da an ki raba musu

- Kayan abincin da ake kwasa sun hada da buhuhunan shinkafa, garin kwaki da kwalayen taliya

Bata gari sun ci karansu ba babbaka ranar Asabar a jihar Plateau yayinda suka fasa dakin ajiya gwamnatin jihar dake Bukuru dake karamar hukumar Jos ta kudu kuma suka debe kayan tallafin Korona da ake ajiye.

Matasan sun yi cincirondo a Jos domin diban kayan tallafin Korona (Bidiyoyi)
Matasan sun yi cincirondo a Jos domin diban kayan tallafin Korona (Bidiyoyi) Hoto: @dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Mun damke mutane 229 cikin wadanda sukayi sace-sace da kone-kone a Legas - Sanwo-Olu

Kalli bidiyoyin da muka gani:

KU KARANTA: Bata gari Musulmai suka kai wa hari yanzu - Majalisar Koli ta Shair'a, NSCIA

A Abuja kuwa, 'yan kasuwa a kasuwar UTC, Area 10, Garki, da kuma mazauna yankin sun cika da fargaba yayin da ƴan sanda ke kokarin dakatar da yan ta'adda daga fasa ma'ajiyar kayyaki a yankin.

'Yan sanda da sauran jami'an tsaro suna ta harba bindiga da barkanon tsohuwa don dakatar da ƴan ta'addan daga fasa ma'ajiyar kayyaki da kayan tallafin Corona ke ciki da sanyin safiyar yau.

Wani mai zane, Segun Stickers, yace an rufe kasuwar UTC da wani babban rukunin shagunan siyayya.

"Yanzu haka muna rufe a cikin kasuwar UTC. Yan sanda suna ta harba bindiga da barkanon tsohuwa don kare mahara daga yunkurin sace kayyakin tallafin Corona a ma'ajiyar dake cikin kasuwar.

"Mutane da dama sun ji rauni a kokarin gujewa maharan, kuma gaba daya yankin suna cikin firgici," ya shaida ta wayar salula.

Wakilanmu suna iya jin karar harbi da kuma murya ana cewa kowa ya rufe shagonsa ya tafi gida.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel