Matasa sun kai farmaki dakin ajiyan kayan talafin Korona, sun debi buhuhunan hatsi

Matasa sun kai farmaki dakin ajiyan kayan talafin Korona, sun debi buhuhunan hatsi

- Satan kayan tallafin Korona ya zama ruwan dare a jihohin Najeriya

- Matasa a jihohin daba-daban sun lashi takobin diban kayan tallafin tun da an ki raba musu

- Wasu sun ce kayan abincin sun fara lalacewa musamman garin kwaki

Bata gari sun ci karansu ba babbaka ranar Asabar a jihar Edo yayinda suka fasa dakin ajiya gwamnatin jihar dake Medical Store Raod kuma suka debe kayan tallafin Korona da ake ajiye.

Matasan da suka yi kokarin fasa dakin ajiyan da safe amma Sojoji suka hanasu, sun samu nasara daga baya kuma suka shiga dakin ajiyan.

Babu wanda aka harba lokacin da suke diban hatsin amma da dama sun ji rauni sakamakon cinkoso.

A jawabin da, Crusoe Osagie, mai magana da yawun gwamnan jihar, Godwin Obaseki, ya saki, ya ce gwamnatin jihar na rabawa mutane kayan abincin tsawon watanni bakwai da suka gabata.

KARANTA: Bamu da gidan zama, an hana mu komai na gado - Daya daga matan marigayi Ado Bayero

Matasa sun kai farmaki dakin ajiyan kayan talafin Korona, sun debi buhuhunan hatsi
Matasa sun kai farmaki dakin ajiyan kayan talafin Korona, sun debi buhuhunan hatsi Credit: @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bata gari Musulmai suka kai wa hari yanzu - Majalisar Koli ta Shair'a, NSCIA

Wannan ya biyo bayan wanda ya faru a Calabar inda matasa afka dakin ajiya kayayyaki da ke Bishop Moynah Street, inda aka ajiye kayan abinci na tallafin annobar korona inda suke ta diban abinda suke so.

Mutanen da suka hada da maza da mata suna ta tururuwa zuwa wurin da kayan abincin suke suna diba a kai.

Gwamnatin jihar ta tara dubunnan kwalayen Indomie da ya kamata a rabawa mutane lokacin dokar kulle na Korona amma har yanzu ba'a raba ba.

Wannan shine kusan jiha ta biyar da matasa zasu shiga dibar tallafin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng