Mayakan Boko Haram sun shiryawa sojoji gadar zare, sun kashe guda 7

Mayakan Boko Haram sun shiryawa sojoji gadar zare, sun kashe guda 7

- Wasu mayakan kungiyar Boko Haram sun shiryawa dakarun rundunar soji a kauyen Doska da ke karamar hukumar Damboa a jihar Borno

- Majiyar soji ta sanar da TheCable cewa an kashe sojoji bakwai tare da raunata wasu goma sha kwai

- Mayakan kungiyar Boko Haram da ke kauyen Doska da kewaye sun yi kaurin suna wajen kadaddamar da harin kwanton bauna a kan dakarun soji

A kalla dakarun rundunar soji bakwai ne suka rasa ransu bayan mayakan kungiyar Boko Haram sun shirya musu gadar zare a Doska, jihar Borno, kamar yadda jaridar TheCable ta wallafa cewa majiyar soji ta tabbatar mata.

TheCable ta rawaito cewa dakarun rundunar soji sun fita faturu ne zuwa yankin Doska a yayin da suka ci karo da mayakan kungiyar Boko Haram sanye da kakin soji da kuma motoci masu dauke da bindigu.

Doska wani kauye ne a tsakanin garin Ajigin da Talata a karamar hukumar Damboa a jihar Borno da jama'a suka kauracewa tun shekarar 2015 bayan mayakan kungiyar Boko Haram sun kwace iko da kauyen.

KARANTA: Sojoji sun sheke Abubakar Haruna, dillalin makaman 'yan bindigar Katsina

Har yanzu kauyen Doska na daga cikin wuraren da mayakan kungiyar Boko Haram keda karfi.

Mayakan Boko Haram sun shiryawa sojoji gadar zare, sun kashe guda 7
Sojojin Najeriya
Asali: Facebook

"Dakarun rundunar sojin sun fita faturu ne zuwa Doska lokacin da suka hadu da mutane a cikin kakin soji da motoci da makaman sojoji, sun ma dagawa sojoji hannu a zuwan sojoji ne daga wani sansanin.

KARANTA: Dalilin da yasa muka yi gum da bakinmu a kan harbe-harben Lekki - Rundunar Soji

"Rundunar sojojinmu ta tsaya tare da gaisawa da wadannan mutane bisa tunanin sojoji ne. Suna yin gaba daga wurin aka kai musu harin kwanton bauna, sai wadancan mayakan suka juyo, suka tarfa sojojinmu, suka bude musu muta ta kowanne bangare.

"Mun rasa sojoji bakwai, guda 17 sun samu munanan raunuka," a cewar majiyar.

Mayakan Boko Haram da ke yankin Doska da kewaye sun yi kaurin suna wajen kaddamar da harin kwanton bauna a kan rundunar soji tare da yin awon gaba da makamansu da sauran kayansu.

Yunkurin jin ta bakin kakakin rundunar soji, Kanal Sagir Musa, a kan lamarin bai samu ba ya zuwa lokacin wallafa rahoto.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel