Garus Gololo ya caccaki Gwamna Samuel Ortom a kan goyon-bayan EndSARS
- Gwamnan Jihar Benuwai Samuel Ortom ya na goyon bayan #EndSARS
- Jagoran APC, Garus Gololo ya dura kan Gwamnan na PDP a dalilin haka
- Gololo ya ce babu aikin da Ortom ya ka ke yi domin gyara jihar Benuwai
Dr. Garus Gololo, daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC, ya maida wa gwamna Samuel Ortom martani a game da kiran da ya yi kwanaki.
Jaridar Leadership ta rahoto Garus Gololo ya na sukar kiran da gwamnan jihar Benuwai ya yi.
Da ya ke magana da ‘yan jarida a birnin Abuja, Garus Gololo ya ce akwai gidadanci da rashin kishin kasa a lamarin gwamnan na Benuwai.
KU KARANTA: Abubuwan da jawabin Shugaban kasa a kan #EndSARS su ka taba
Gololo ya ce babu cigaba a Benuwai ko kadan, don haka ya bukaci Ortom ya maida hankali wajen kawo canji a jiharsa kamar sauran takwarorinsa.
“Abin takaici ne, maimakon ya maida hankali wajen yadda zai gyara jiharsa da babu cigaba, Ortom ya damu da goyon-bayan matasa su cika tituna.”
“Ba na ganin laifinsa. A lokacin da sauran gwamnoni su ke gyara jihohinsu, babu abin da Ortom ya ke yi sai fakewa da rikicin makiyaya.” Inji Gololo.
“Ya jawo matasa ya koya masu sana’a da abin yi. Abin takaici shi ne babu masana’antu a jihar.”
KU KARANTA: Gwamnonin Arewa sun yi tir da masu zanga-zangar #EndSARS

Asali: UGC
Dr. Gololo ya kuma caccaki gwamnatin Ortom kan rashin biyan albashin ma’aikata da fansho, ya ce wannan ya kamata matasa su yi wa zanga-zanga.
“Buhari ya rusa SARS, abin da na ke so matasan Benuwai su yi wa zanga-zanga shi ne rashin biyan albashi da fansho, dole a daina wannan.”
Kwanakii kun ji cewa gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bukaci tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya nemi afuwarsa.
Gwamnan ya yi alkawari idan Oshiomhole yayi hakan, to za suyi sulhu a shari'ar da su ke yi.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng