Jan-kunne, a koma-aiki, sabon albashi da sauran abubuwan da Buhari ya fada

Jan-kunne, a koma-aiki, sabon albashi da sauran abubuwan da Buhari ya fada

- A jiya da yamma Shugaban kasa ya fito ya yi wa al’ummar Najeriya jawabi

- Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi a dakatar da zanga-zangar haka nan

- Gwamnati ta yi alkawarin kare ran al’umma da kara albashin jami’an tsaro

A ranar Alhamis, shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa ‘yan kasa jawabi a karon farko bayan zanga-zangar #EndSARS ya fara daukar wani sabon salo.

Jaridar Daily Trust ta tattaro manyan kanun da ke cikin jawabin da shugaban kasar ya yi a jiya.

Mun tsakuro wasu daga cikinsu:

1. Akwai masu wata manufa

Shugaban kasar ya yi gargadi cewa akwai wasu bata-gari da su ka shige cikin rigar #EndSARS domin su kawo tarzoma. Ya kuma fada wa sauran kasashe su yi bincike, kafin su tsoma-baki.

KU KARANTA: Zanga-zanga: Gwamnan Legas ya ce bai yi waya da Buhari ba

2. Danyen aikin SARS

Muhammadu Buhari ya yarda cewa da gaske dakarun SARS su na cin zarafin al’ummar Najeriya.

3. Damar zanga-zanga

Shugaban Najeriyar ya ce duk wani ‘dan kasa ya na da damar fita zanga-zanga, amma bai da ikon ya shiga hakkin sauran jama’a.

4. Bukatun #EndSARS

Buhari ya ji kukan masu zanga-zangar #EndSARS, ya ce don haka aka ruguza sashen, sannan aka kama hanyar biyan sauran bukatun.

5. Duka wa wada ba gajiya wa

A jawabin shugaban kasar, ya ce gaggawar dakatar da aikin SARS da aka yi, ya sa wasu a Najeriya su na yi wa gwamnati kalon rauni.

6. Abin takaici

Babu dalilin barna da ta’adin da wasu tsageru su ka rika yi da sunan #EndSARS inji shugaban kasar.

KU KARANTA: Kungiyar EU ta bukaci Buhari ya cika alkawarin da ya yi na #EndSARS

Jan-kunne, a koma-aiki, sabon albashi da sauran abubuwan da Buhari ya fada
Shugaba Buhari Hoto: Twitter/@MBuhari
Asali: Twitter

7. Sabon tsarin albashin jami’an tsaro

Gwamnatin tarayya ta bada umarnin ayi maza a shigo da sabon tsarin albashin jami’an tsaro.

8. Kokarin gwamnatin APC

Babu gwamnatin da ta yi kokarin yaki da talauci a tarihin Najeriya irin ta mu inji Buhari.

9. Ya isa haka nan

Muhammadu Buhari ya yi kira ga matasa su canza salo, su daina zanga-zanga domin ya ji kukansu.

10. A koma bakin-aiki

Daga cikin abin Buhari ya fada wa ‘Yan kasa shi ne a koma bakin-aiki, sannan jami’an tsaro su kare rayuka.

Dama tun a jiya da rana, kun ji cewa shugaba Muhammadu Buhari zai dauki muhimmin mataki game da matsalar tsaro. Janar Babagana Monguno ya bayyana wannan.

Ya yi wa ‘Yan Najeriya albishir kafin shugaban kasa ya yi bayani kan zanga-zangar #EndSARS.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel