Da ɗuminsa: Ɓata gari sun sake bankawa ofishin ƴan sanda wuta a Lagos

Da ɗuminsa: Ɓata gari sun sake bankawa ofishin ƴan sanda wuta a Lagos

- Wasu bata gari sun sake kona ofishin yan sanda a yakin Ojodu da ke jihar Lagas

- Lamarin ya afku ne a yau Alhamis, 22 ga watan Oktoba

- Ana dai ci gaba da samun tashe-tashen hankula a fadin jihar a yayinda ake zanga-zangar ruguza rundunar yan sandan SARS

Wasu yan iska da ake zaton yan daba ne sun cinna wa ofishin yan sanda na Ojodu da ke jihar Lagas wuta.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa yan daban sun sha karfin jami’an tsaro da ke wajen kafin suka cinna wa ofishin wuta.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamnonin Arewa sun shiga taron gaggawa

Da ɗuminsa: Ɓata gari sun sake bankawa ofishin ƴan sanda wuta a Lagos
Da ɗuminsa: Ɓata gari sun sake bankawa ofishin ƴan sanda wuta a Lagos Hoto: PremiumTimesng
Asali: UGC

Lamarin ya afku ne a yau Alhamis, 22 ga watan Oktoba, yayinda ake ci gaba da zanga-zangar neman a ruguje rundunar SARS.

Akalla ofishin yan sanda guda takwas aka kona kurmus a fadin jihar a ranar Laraba, 22 ga watan Oktoba.

KU KARANTA KUMA: Da ɗuminsa: Buhari na jagorantar zaman majalisar tsaro ta ƙasa yanzu

A halin da ake ciki, mun ji a baya cewa Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, a ranar Alhamis, 22 ga watan Oktoba, ya bayyana ranar da zai cire kullen da yasa a jihar Legas.

A wata hira da gidan talabijin din Arise suka yi da gwamnan, ya ce za'a cigaba da shige da fice a jihar daga ranar Juma'a, 23 ga watan Oktoba.

Sanwo-Olu yace zai aiwatar da hakan matsawar rikicin ya yi kasa.

A cewarsa, "Matsawar masu zanga-zangar EndSARS suka bar tituna, zuwa gobe zan saki kullen, yadda al'amura zasu koma yadda suke."

Har wa yau, fitaccen marubuci, Farfesa Wole Soyinka, ya yi kira ga gwamnonin da suka sa kulle a jihohin su saboda rikicin SARS da su yi gaggawar dakatar da sojojin da gwamnatin tarayya ta tura jihohin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel