Ohaneze Ndigbo, babbar kungiyar kabilar Igbo, ta juyawa Nnamdi Kanu baya

Ohaneze Ndigbo, babbar kungiyar kabilar Igbo, ta juyawa Nnamdi Kanu baya

- Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB ya fitar da wani sautin murya da ya haddasa cece-kuce a tsakanin kabilun Igbo da Yoruba

- A cikin faifan sautin muryar, Nnamdi Kanu ya bukaci matasan kabilar Igbo su mamaye jihar Legas tare da tsayar da al'amura cak

- Sai dai, kungiyar Ohanaeze Ndigbo, ta mayar da martani a kan kalaman Kanu da suka fara fusata matasan kabilar Yarabawa

Babbar Ƙungiyar kabilar Igbo, Ohanaeze Ndigbo, ta nesanta kanta da sauran al-ummar Igbo daga kalaman da shugaban ƙungiyar ƴan asalin Biafra (IPOB), Mazi Nnamdi Kanu, ya furta a kan lalata dukiyoyin al-ummar yarbawa a jihar Lagos.

A wani jawabi da shugaban ƙungiyar da shugaban ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo, Chief Nnia Nwodo, ya fitar ya ce ƙungiyar Ohanaeze bata ji daɗin kalaman ɓatanci da fushi da Kanu ya yi ba.

Kungiyar ta barranta kanta da kuma al-ummar Igbo daga dukkan kalaman da Kanu ya yi akan zanga-zangar neman kawo ƙarshen rundunar SARS a jihar Legas, kamar yadda aka ji a faifan muryarsa da ke yawo a dandalin sada zumunta

DUBA WANNAN: 'Kune fa manyan gobe'; Bidiyon yadda sojoji su ka kwantar da murya don lallaba ma su zanga-zanga

Hakan na kunshe ne a cikin jawabi mai taken; Zanga-zangar kawo ƙarshen rundunar SARS"; Matsayar ƙungiyar Ohanaeze kan iƙirarin lalata dukiyar al-ummar Yarbawa.''

A cewar jawabin, ''hankalin Ohanaeze Ndigbo, ƙungiyar al'adu da kuma siyasa ta al-ummar Igbo a faɗin duniya, ya kawo kan lamarin ne bayan wata ƙungiyar Yarabawa mai tasowa wacce ake kira Apapo O'Odua Koya (AOKOYA) sun fidda sanarwar danganta faruwar lamarin da matasan kabilar Igbo.

Ohaneze Ndigbo, babbar kungiyar kabilar Igbo, ta juyawa Nnamdi Kanu baya
Ohaneze Ndigbo, babbar kungiyar kabilar Igbo, ta juyawa Nnamdi Kanu baya
Asali: UGC

''Kalaman na su abin ƙyamata ne sosai saboda akwai rashin gaskiya a cikin jawaban da suka fitar.

''Wannan wata maƙarƙashiya ce ƙullalliya don tarwatsa daɗaɗiyar dangatakar ta ke tsakanin al-ummar Yarabawa da Igbo.

DUBA WANNAN: Rundunar soji ta kama sojan da ke goyon bayan ma su zanga-zanga

"Al'ummar Igbo basa tare da kalaman Nnamdi Kanu, mun dade muna jin dadin kyakyawar alakar da ke tsakaninmu da kabilar Yarabawa, ba zamu bari wani ko wani abu ya lalata aminci da zumuncin da ke tsakaninmu ba," a cewar wani bangare na jawabin.

A cikin wani faifan sautin murya da ke yawo a dandalin sada zumunta, an ji Nnamdi Kanu ya na bawa 'yan kabilar Igbo umarnin su mamaye Lagos, su tsayar da harkokin kasuwanci da na gwamnatin jihar a yayin da ya ke gargadinsu da kar su lalata dukiyoyi a jihohin Enugu da Imo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel