Masu kwangila a Najeriya sun biyo mu bashin N392bn inji Tunde Fashola

Masu kwangila a Najeriya sun biyo mu bashin N392bn inji Tunde Fashola

- ‘Yan kwangila su na bin Gwamnatin Tarayya abin da ya kusa Naira biliyan 400

- Ministan ayyuka da gidajen Najeriya, Raji Babatunde Fashola ya bayyana haka

- Babatunde Fashola ya ce ana bukatar N6.6tr domin a kammala titunan tarayya

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ana bin ta tarin bashin kudi na ayyukan ginin hanyoyi fiye da 700 da ake yi a fadin jihohin kasar nan.

Ministan ayyuka da gidaje na kasa, Raji Babatunde Fashola SAN, ya ce kudin da ake bin gwamnatin tarayya ya tashi a Naira biliyan 392.

Daily Trust ta ce Babatunde Fashola ya bayyana haka ne a lokacin da ya bayyana gaban majalisar dattawa domin kare kasafin kudin ma’aikatarsa.

KU KARANTA: #EndSARS: Yadda aka kai wa Shugaba Buhari munafuncin Tinubu

Jaridar ta ce Ministan ya tsaya ne gaban kwamitin ayyuka na majalisar dattawa a ranar Laraba.

Mai girma Ministan ya ce bashin da ke kan gwamnatin Najeriya ya zarce gaba daya duk abin da aka yi kasafi a matsayin kudin aikin tituna a 2021.

A dalilin haka, Ministan ya ce gwamnati ta daina bada sababbin kwangiloli, sai dai a maida hankali domin kammala ayyukan da aka riga aka bada.

Babatunde Fashola ya ce gwamnati ta na bukatar Naira tiriliyan 6.62 domin ta iya daukar nauyin duka ayyukan tituna 711 da ake yi a jihohin kasar.

KU KARANTA: Dole a ba Ibo titikin Shugaban kasa a 2023 ko kuma... – Shugabannin PDP

Masu kwangila a Najeriya sun biyo mu bashin N392bn inji Tunde Fashola
Raji Fashola Hoto: guardian.ng/news/resign-if-you-cant-cope-senate-tells-fashola
Asali: UGC

Ministan ayyuka da gidajen ya koka a majalisa kan karancin kudi da su ka hana yin ayyukan.

Majalisa ta bakin Sanata Adamu Aliero ta nemi ayi amfani da tulin kudin fansho domin wadannan ayyuka, Fashola ya ce hakan ya zarce huruminsa.

A yau ne kuma ku ka ji cewa Majalisar wakilan tarayya za ta yi bincike a kan zargin wawurar kudin Coronavirus da wasu badakala aka tafka a ma'aikatu.

Babban mai binciken kudin kasa ya na zargin an wawuri kudi a NBET, NIMET da NDDC.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel