MNJTF: ‘Yan ta’addan Boko Haram da ISWAP 120 sun mika wuya a tafkin Chadi

MNJTF: ‘Yan ta’addan Boko Haram da ISWAP 120 sun mika wuya a tafkin Chadi

- ‘Yan ta’addan kungiyar Boko Haram da ISWAP su na mika kansu gaban Sojoji

- MNJTF ta ce sojojin 'yan ta’adda sama da 120 sun mika wuya a watannin nan

- Janar Ibrahim Yusuf ya bayyana haka wajen wani taro da aka yi a kasar Chadi

Dakarun sojojin hadin-gwiwa na MNJTF sun ce fiye da mayakan Boko Haram da kungiyar ISWAP su ka mika wuya a yankin tafkin Chadi.

Rundunar hadin-gwiwar da aka kafa daga kasashen Benin, Kamaru, Chad, Nijar da Najeriya ta bada labarin gagarumar nasara da ta samu.

Jaridar The Cable ta ce MNJTF ta yi wannan bayani ne ta bakin jagoranta, Manjo-Janar Ibrahim Yusuf, a wajen wani taro na kara wa juna sani.

KU KARANTA: Babu ruwanku da zanga-zangar #EndSARS, mun ga Boko Haram – Buni

Kamar yadda rahoton ya bayyana, an gudanar da wannan taro ne a babban birnin Chad, Djamena.

Janar Ibrahim Yusuf ya bayyana cewa an shafe watanni uku sojojin kungiyoyin ‘yan ta’addan na Boko Haram da ISWAP su na mika kansu ga sojoji.

Sojan ya ce dabarun da su ka shigo da su na dakile hanyoyin jan hankalin jama’a da ‘yan ta’addan su ke yi, ya taimaka wajen mika wuyar da ake yi.

Yusuf ya ce yanzu dakarun sojojin MNJTF sun kammala mika wadannan ‘yan ta’adda da na-kusa da su zuwa hannun hukumomin gwamnatin tarayya.

KU KARANTA: Zanga-zanga: Hillary Clinton ta tsoma baki game da abin da ya faru a Legas

MNJTF: ‘Yan ta’addan Boko Haram da ISWAP 120 sun mika wuya a tafkin Chadi
Shugabannin MNJTF Janar Ibrahim Yusuf Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC

Rundunar gamayyar kasashe Afrika ta yamman su na kokarin kawo zaman lafiya a yankin tafkin

Sojojin sun raina dabarun sadarwar jami’anta, don haka ne aka shirya wannan taro domin a kara wa juna sani, kamar yadda Janar Yusuf ya bayyana.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi kira ga al'ummar Borno da su dauki a ranar Litinin.

Babagana Umara Zulum ya bukaci hakan ne domin a yaki ta'addanci da ibada da bautar Allah.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel