Bata gari sun kai hari ofishin NDLEA, sun kwashe wiwi da muggan kwayoyi

Bata gari sun kai hari ofishin NDLEA, sun kwashe wiwi da muggan kwayoyi

- Bayan diban shinkafa a dakin ajiyan Kwastam jiya, bata gari sun sake kai hari ofishin NDLEA

- Matasan basu daina fita ba duk da dokar hana fitan da gwamna Obaseki ya sa

Wasu bata garin jama'a sun yi amfani da sunan zanga-zangan #EndSARS wajen kai hari ofishin hukumar hana ta'amuni da muggan kwayoyi watau NDLEA ranar Laraba a jihar Edo.

An tattaro cewa matasan bayan kwashe buhuhunan ganyen wiwi da wasu muggan kwayoyi sannan suka bankawa dakin ajiyan wuta.

Bata garin sun kai hari ofishin hukumar dake Sakpoba dake karamar hukumar Ikpoba Okha na jihar yayinda Sojoji suke sintiri a jihar.

Wasu mazauna unguwasr sun bayyana cewa yan bata gari ne suka kai hari ofishin ba masu zanga-zanga ba.

A cewar majiyar Daily Trust, ofishin NDLEA ba wani waje bane da akwai kayayyakin alfanu da mutumin kirki zai shiga illa bata gari kuma don satan kayan maye da jami'an hukumar suka kwace.

Bayan haka, majiya da gidan yan sanda ya bayyana cewa bata garin sun rikide da masu zanga-zanga ne wajen barnan.

KARANTA WANNAN: Matasa sun bankawa gidan talabijin mallakin Tinubu, TVC News, wuta

Bata gari sun kai hari ofishin NDLEA, sun kwashe wiwi da muggan kwayoyi
Bata gari sun kai hari ofishin NDLEA, sun kwashe wiwi da muggan kwayoyi
Asali: UGC

KARANTA NAN: Rikicin #EndSARS: Jerin wurare 23 da bata gari suka kai hari ko bankawa wuta

A jiya mun ruwaito muku cewa wasu bata gari a ranar Talata sun fasa dakin ajiyar hukumar hana fasa fasa kwabri watau Kwastam dake garin Benin City da sunan zanga-zangan #EndSARS.

An tattaro cewa bata garin sun fasa dakin ajiyan dake Ikpoba da yammacin Talata kuma sukayi awon gaba da kayayyakin abinci da wasu kayayyaki, Daily Trust ta ruwaito.

Hakazalika an tattaro cewa mutan unguwa suka samu labarin abinda ke faruwa, sun garzaya wajen domin samun nasu rabon na kayan masarufin.

An ga bata garin da mazaunan suna awon gaba da buhuhunan shinkafa da was kayayyaki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel