EndSARS: Shugaban NSCDC ya saka dokar ta-baci a kan kadarorin gwamnati da ababen more rayuwa

EndSARS: Shugaban NSCDC ya saka dokar ta-baci a kan kadarorin gwamnati da ababen more rayuwa

- Bayan tashin tarzoma a jihohin Najeriya sakamakon zanga-zangar rushe SARS, matakan tsaro na iyakar kokarin su wurin ganin sun bayar da kariyar da ta dace

- Kwamanda janar na NSCDC, Abdullahi Gana Muhammadu ba'a barshi a baya ba, inda ya tara jami'ansa a hedkwatarsu dake Abuja don taron gaggawa

- Ya umarci duk wani Kwamanda da ke fadin kasar nan da ya tura jami'ansa dake jihohi don tabbatar sun taimaka wurin kulawa da dukiyoyin gwamnati, don asarar gwamnati asarar kowa ce

Bayan tayar da tarzomar rushe SARS a jihohin da dama na kasar nan, Kwamanda janar na NSCDC, Abdullahi Gana Muhammadu, ya yi kiran gaggawa a kan ma'aikatun gwamnati.

Ya umarci duk wasu kwamandojin kasar nan da su tura jami'ansu don bayar da kariya ga duk wasu ma'aikatu da dukiyoyin da ke kusa da su don gudun asara da kuma lalacewar al'amuran gwamnati.

Kakakin NSCDC, Emanuel Okeh, ya ce Kwamanda janar dinsu ya bayar da umarnin ne a hedkwatarsu da ke Abuja, yayin da yake yi musu bayani a kan yadda harkar tsaro ta tabarbare a kasar nan.

KU KARANTA: Sarauniya Amina: Jarumar da ke kashe duk namijin da ya kwanta da ita

Ya dage wurin nuna musu cewa lallai ma'aikatun kasar nan suna cikin hatsari a wannan lokacin na tsanani, kuma 'yan ta'adda na iya kai musu farmaki a duk damar da suka samu.

Yace wajibi ne a gujewa hakan, don idan asara ta samu gwamnati, ta samu kowa, don haka hakkin kowa ne kare dukiyar kasa.

Ya ce wajibi ne kula da matatu, titunan motoci, titunan jirgin kasa, gadoji, gidajen talabijin da sauransu.

Ya kuma shawarci jama'a a kan kiyayewa a hanyarsu ta neman abinci don kada tarzomar ta shafesu.

EndSARS: Shugaban NSCDC ya saka dokar ta-baci a kan kadarorin gwamnati da ababen more rayuwa
EndSARS: Shugaban NSCDC ya saka dokar ta-baci a kan kadarorin gwamnati da ababen more rayuwa. Hoto daga @Vanguard
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotunan kyawawan gidaje 7 na miliyoyin daloli mallakin Donald Trump

A wani labari na daban, bata-garin matasa a ranar Laraba sun banka wa gidan iyayen gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, wuta. Gidan yana kan titin Omididun inda suka dinga jifansu da duwatsu.

Gwamna Sanwo-Olu ya saka dokar ta baci ta sa'o'i 24 a jihar sakamakon zanga-zangar EndSARS a ranar Talata. Daga bisani sojoji sun shiga lamarin, abinda ya kawo mutuwar a kalla mutane 7 wadanda da yawansu matasa ne.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel