Zargin handame miliyan 950: Kotu ta wanke Shekarau

Zargin handame miliyan 950: Kotu ta wanke Shekarau

- Kotun daukaka kara da ke zama a jihar Kano ta wanke Sanata Ibrahim Shekarau soso da sabulu daga zargin da ake masa

- EFCC ce ta gurfanar da Shekarau kan zargin yin sama da fadi kan kudade naira miliyan 950 na zaben Shugaban kasa na 2016

- Ana zarginsa da karbar kudin daga hannun tsohuwar ministar man fetur, Diezani Alison

Wata kotun daukaka kara da ke Kano ta wanke tsohon gwamnan jihar, Sanata Ibrahim Shekarau daga zargin da ake masa na yin babakere a kan kudi naira miliyan 950, jaridar Aminiya ta ruwaito.

Hukumar yaki da cin hancin da hana yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ce ta gurfanar da shi kan zargin karbar kudin zabe a 2015.

Ana zargin ya karbar kudin ne daga hannun tsohuwar ministar man fetur, Deizani Alison Madueke a lokacin gwamnatin tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Zargin handame miliyan 950: Kotu ta wanke Shekarau
Zargin handame miliyan 950: Kotu ta wanke Shekarau Hoto: @vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Bidiyon yadda ƴan sandan Faransa suka ga akushin tsafi a harabar ofishin jakadancin Nigeria da ke ƙasar

EFCC na zargin Shekarau da tsohon ministan harkokin kasashen waje, Ambasada Aminu Wali da Mansur Ahmad da karbar kudaden da aka raba wa wakilan jam’iyyar PDP a jihohi, inda ake zargin tsohon gwamnan da karbar naira miliyan 25.

A yanzu haka, magoya bayan tsohon gwamnan a kafafen soshiyal midiya na cike da murnar nasarar da suka samu na wanke jagoran nasu daga zargin da ake yi masa.

KU KARANTA KUMA: Yan daba sun kai hari sakatariyar APC a jihar Ondo

Idan za ku tuna, a baya wata babbar kotu dake zaune a Kano ta nemi tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau, Ambasada Aminu Wali da kuma Injiniya Ahmed Mansur fita daga Najeriya.

Kotun ta bayyana hakan ne bayan zargin su da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ke yi akan fitar da miliyan 950 ta hanyar da bata dace ba.

Kotun ta kuma bukaci Sanatan da mukarrabansa akan su bayar da takardunsu na fita kasar waje, domin a cigaba da bincike a kansu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel