Yan daba sun kai hari sakatariyar APC a jihar Ondo

Yan daba sun kai hari sakatariyar APC a jihar Ondo

- Wasu da ake zaton bata gari ne sun kai farmaki sakatariyar jam’iyyar APC mai mulki a jihar Ondo

- Hakan na zuwa ne bayan gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu ya saka dokar hana fita a jihar sakamakon zanga-zangar EndSARS

- Sai dai kakakin jam’iyyar a jihar, ya zargi jam’iyyar adawa da PDP kan harin

Wasu bata gari sun kai hari sakatariyar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a garin Akure, babbar birnin jihar Ondo.

Lamarin ya afku ne a yau Laraba, 21 ga watan Oktoba, duk da dokar hana fita da Gwamna Oluwarotimi Akeredolu ya sanya a fadin jihar.

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Ƴan ta'adda sun kashe ƴan sanda biyu yayin da suka bankawa ofishin rundunar wuta a Oyigbo

Yan daba sun kai hari sakatariyar APC a jihar Ondo
Yan daba sun kai hari sakatariyar APC a jihar Ondo Hoto: @SaharaReporters
Asali: Twitter

Kakakin jam’iyyar APC a jihar, Alex Kalejaiye, wanda ya tabbatar da harin a wayar tarho, ya ce zanga-zangar da ake yi yanzu ba wai na kawo karshen rundunar SARS bane, jaridar The Nation ta ruwaito.

Kalejaiye ya ce jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ce ta shirya lamarin.

A wani labarin, jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ya ce ba zai taba kasance da hannu a cikin kowani irin barna da ta’addanci ba.

Tinubu na martani ne ga harin daren ranar Talata, 20 ga watan Oktoba, wanda aka gano jami’an tsaro suna bude wuta a kan masu zanga-zangar EndSARS a Lekki da ke Lagas.

Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya yi magana ne a wata hirar waya da Channels TV a safiyar ranar Laraba, jaridar Punch ta ruwaito.

Tinubu ya yi watsi da matakin da ake zargin rundunar sojin da dauka, cewa, ta yaya za su yi amfani da harsasai?

“Ba zan taba kasancewa a cikin kowani irin barna ba. Ba zan taba kasancewa da hannu a ciki ba,” in ji shi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel