Sheikh Bauchi ya bukaci Gwamnati ta zauna da masu zanga-zanga a Najeriya

Sheikh Bauchi ya bukaci Gwamnati ta zauna da masu zanga-zanga a Najeriya

- Dahiru Bauchi ya bukaci masu zanga-zanga su yi hakuri su zauna da Gwamnati

- Shehin ya yi kira ga gwamnati ta duba bukatu da jama’a su ke nema cikin lalama

- Malamin ya ce ba za a samu zaman lafiya idan kowane bangaren ya sa karfi ba

Babban shehin malamin addinin musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya yi kira ga gwamnati da al’umma game da zanga-zangar da ake ta yi.

Dahiru Usman Bauchi ya yi wata hira da BBC Hausa a ranar Laraba inda ya ja-kunnen ‘yan kasa.

“Mu na jawo hankalin gwamnati, ta lura da hakkin mutanen kasa da ta ke mallaka. Mu na fatan ta samu masu ba ta shawarar gaskiya, kuma ta dauka.”

Shehin ya ce: “Amma a bar abin ya na tafiya haka, ba zai yi mana kyau ba. Gwamnati ta duba hakkin mutane, ta biya masu bukatunsu da ta ke iya wa.”

KU KARANTA: Clinton da Rihanna sun koka da kashe masu zanga-zanga

Har ila yau, malamin ya ja-kunnen masu zanga-zanga. “Su kuma mutanen kasa su bi a hankali, idan su ka cigaba da haka, duk komai zai lalace.”

Jagoran darikar Tijjaniyan ya ke cewa: “Za a zo a rasa abin da aka raina na zaman lafiya.”

A daidai wannan lokaci kungiyar Lauyoyin Afrika ta na barazanar za ta kai karar Gwamnatin Tarayya a dalilin harbe-harben da aka yi Lekki a jiya.

Da aka tambayi Sheikh Bauchi game da abin da ya kamata hukuma ta yi, sai ya ce:

KU KARANTA: Gwamnatin Legas ta bayyana abin yi bayan an harbe 'yan zanga-zanga

Sheikh Bauchi ya bukaci Gwamnati ta zauna da masu zanga-zanga a Najeriya
BUHARI da SHEIKH DAHIRU BAUCHI Hoto: Solacebase
Asali: UGC

“Abin da zan ce shi ne gwamnati ta na da kunnuwa da idanu, kunnuwanta su na jin abin da ‘yan kasa su ke fada, idanunta na kallon abinda ake damuwa da shi.”

Daga cikin abubuwan da ya ce ake damuwa da shi akwai rashin tsaro da zaman lafiya, tsadar kayan abinci da rashin abin yi, don haka ya ce ayi zaman sulhu.

Shehin ya bukaci masu zanga-zanga su dakata domin a sasanta, ta yadda gwamnati za ta biya masu bukatunsu, ya gargadi gwamnatin kasar a kan amfani da karfi.

Shugaban Majalisar wakilai ya bada sharudan amincewa da kasafin da Buhari ya gabatar. Ya ce dole kasafin 2021 ya kunshi diyyar #EndSARS da bukatun ASUU.

Majalisar tarayya ta ce fau-fau ba za ta amince da kundin kasafin kudin 2021 ba sai an yi wannan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel