Rundunar soji ta kama sojan da ke goyon bayan ma su zanga-zanga

Rundunar soji ta kama sojan da ke goyon bayan ma su zanga-zanga

- Rundunar sojin Najeriya ta fitar da sanarwar kama jami'inta da ya nuna goyon bayansa ga zanga-zangar neman rushe rundunar SARS

- Matashin sojan mai suna Harrison Friday ya rufe fuskarsa da kyalle kafin ya nadi faifan bidiyon nuna goyon baya ga ma su zanga-zanga

- Sai dai, hakan bai hana rundunar soji ta sanar da cewa ta gane jami'in ba, kuma har ma ta kama shi da aikata laifi ta hanyar amfani da yanar gizo

An zargi wani soja, Harrison Friday, mai mukamin 'lance corporal', da aikata laifi ta hanyar amfani da yanar gizo bayan ya nuna goyon bayansa ga ma su zanga-zangar neman a rushe rundunar SARS da kawo karshen zaluncin jami'an 'yan sanda.

An shiga kwanaki na 13 da fara zanga-zangar neman a gudanar da garambawul a rundunar 'yan sanda ta kasa (NPF).

Ma su zanga-zanga sun ci alwashin cewa ba za su bar kan tituna ba har sai an biya dukkan bukatunsu da sharudan da suka gindaya.

Rundunar soji ta kama sojan da ke goyon ma su zanga-zanga
Harrison Friday
Asali: Twitter

A kokarinsa na tofa albarkacin bakinsa a kan zanga-zangar, Friday ya nadi faifan bidiyo tare da rokon abokansa sojoji a kan kar su yi aiki ko biyayya ga duk wani umarni daga sama a kan su illata 'yan kasa da sunan kwantar da zanga-zanga.

KARANTA: A karshe: Buhari ya yi jawabi a kan zanga-zangar ENDSARS, ya roki matasa cikin lafazi mai sanyi

"Ni shawarata zuwa ga abokan aikina sojoji ne, kar ku bari a mayar da ku wawaye ko a yi amfani da ku, mu ma matasa ne, a saboda haka duk abinda ya shafi matasa ya shafemu," kamar yadda Friday ya fada a bidiyon da ya nada bayan ya rufe fuskarsa da kyalle.

"Na san za a yi amfani da sojoji domin razana ma su zanga-zanga. Ku sani cewa idan ku ka dauki doka a hannunku, ku ka amince ku harbi fararen hula, alburushin da ya fita daga bindigarka zai iya zuwa ya samu dan uwanka ko 'yar uwarka.

"Ku tuna cewa duk wannan zanga-zanga da matasa ke yi za ta yi mana amfani gaba daya. Da Najeriya tana samun cigaba, babu mai ajiye aikinsa ya fice ya bar kasar domin neman rayuwa mai ma'ana a kasashen ketare.

"Da ana biyan sojoji da fararen hula albashi mai kyau, ba za su yi sha'awar ajiye aikinsu su bar kasa ba," a cewar Friday.

KARANTA: Bidiyon yadda soji suka ragargaji sansanin horas da mayakan ISWAP a jihar Borno

Sai dai, rundunar soji ta ce ''Friday ya boye fuskarsa a cikin kyalle domin ya aika laifi ta hanyar amfani da yanar gizo.''

A cikin wani sako da rundunar soji ta fitar ranar Laraba, ta bayyana cewa kama Friday na daga cikin aiyukan atisayen 'hawayen kada' da rundunar soji ta kaddamar a makon jiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel