Wata sabuwa: Ƴan ta'adda sun kashe ƴan sanda biyu yayin da suka bankawa ofishin rundunar wuta a Oyigbo

Wata sabuwa: Ƴan ta'adda sun kashe ƴan sanda biyu yayin da suka bankawa ofishin rundunar wuta a Oyigbo

- Wasu da ake zargin yan daba ne sun kai farmaki ofishin ya sanda da ke Oyigbo a jihar Ribas

- Har ila yau miyagun sun halaka yan sanda biyu yayinda suka cinnna wa ofishin wuta

- Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar al'amarin

Akalla jami’an yan sanda biyu ne suka rasa ransu yayinda wasu da ake zargin yan ta’adda ne suka cinna wa ofishin yan sanda wuta a Oyigbo, karamar hukumar Oyigbo ta jihar Ribas.

Wani idon shaida, Cif Bright Ogbomudia, ya fada ma jaridar Daily Trust cewa miyagun sun kai farmaki ofishin yan sandan yanki a titin Port Harcourt/Aba a safiyar ranar Laraba.

Sannan suka cinna ma motar yan sandan da aka ajiye a kofar ofishin wuta kafin suka sanya wa ainahi ginin ma wuta.

Idon shaidan ya bayyana cewa wani jami’in dan sanda wanda ya kasance direban da ke tuka motar, na a cikin motar lokacin da aka cinna mata wuta, inda ya kone kurmus.

Ya bayyana cewa yan iskan sun harbe wani jami’in dan sanda har lahira yayinda dukkanin jami’an rundunar suka ci na kare.

Wata sabuwa: Ƴan ta'adda sun kashe ƴan sanda biyu yayin da suka bankawa ofishin rundunar wuta a Oyigbo
Wata sabuwa: Ƴan ta'adda sun kashe ƴan sanda biyu yayin da suka bankawa ofishin rundunar wuta a Oyigbo Hoto: @thesunnigeria
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Harbin masu zanga zanga a Lekki: Gwamna Sanwo-Olu ya roƙi yafiyar ƴan Legas

“Abun ya faru a tsakar daren ranar Talata lokacin da muka fara jin karar harbin bindiga.

“Harsasai na ta yawo ta kowani lungu sannan muka nemi mafaka saboda gidana na kusa sosai da ofishin yan sandan.

“Na ji suna ihun cewa sun zo ramuwar gayya ne a kan kisan masu zanga-zangar da basu ji ba basu gani ba a Lagas.

“Sun sanya wa motar silke na yan sandan da ke fake a gaban ofishin wuta tare da direban motar a ciki.

“Sun yi ta harbi a yayin shigarsu ofishin yan sandan sannan suka cinnawa ginin wuta.

“Sun kuma harbe wani dan sanda har lahira.

“Ba mu yi bacci ba da daddare.

“Dukkanin jami’an yan sandan cikin ofishin da na bariki sun tsere,” in ji shi.

KU KARANTA KUMA: Zangazangar #EndSARS: Ba bu hannuna a cikin harbe-harben da aka yi a Lekki - Tinubu

Kakakin rundunar yan sandan jihar Ribas, Nnamdi Omoni, ya tabbatar da labarin.

Ya bayyana cewa kwamishinan yan sanda, Joseph Mukan, zai ziyarci ofishin yan sandan don gane ma idanunsa.

A gefe guda, rundunar 'yan sandan jihar Legas, a ranar Laraba ta ce ta kama daya daga cikin wadanda suka kai hari a wasu bankuna a unguwar Lekki a daren ranar Talata.

The Nation ta ruwaito cewa 'yan sandan sun bayyana cewa sun gano wasu kudade da ba a bayyana adadinsu ba a tare da shi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng