Harbin masu zanga zanga a Lekki: Gwamna Sanwo-Olu ya roƙi yafiyar ƴan Legas

Harbin masu zanga zanga a Lekki: Gwamna Sanwo-Olu ya roƙi yafiyar ƴan Legas

- Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ba mutanen Lagas hakuri cewa su tona su binne domin wanzuwar zaman lafiya

- A wani jawabi a jihar gwamnan ya bayar da hakuri a kan bude wutar da aka yi wa masu zanga-zanga a kofar shiga Lekki

- Sai dai, Sanwo-Olu ya bayyana cewa babu wanda ya mutu a yayin bude wutar sabanin yadda ake ta yayatawa

Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ba mazauna jihar Lagas hakuri sakamakon wuta da jami’an tsaro suka budewa masu zanga-zangar lumana a yankin Lekki a ranar Talata, 20 ga watan Oktoba, wanda aka ce ya yi sanadiyar mutuwar wasu.

A wani jawabi na fadin jiha da ya yi a ranar Laraba, 21 ga watan Oktoba, wanda Legit.ng ta bibiya, Gwamna Sanwo-Olu ya roki fusatattun matasan da su bayar da damar dawo da zaman lafiya.

Gwamnan ya ci gaba da bayyana cewa wannan shine lokaci mafi muni a tarihin jihar da Najeriya baki daya.

Harbin masu zanga zanga a Lekki: Gwamna Sanwo-Olu ya roƙi yafiyar ƴan Legas
Harbin masu zanga zanga a Lekki: Gwamna Sanwo-Olu ya roƙi yafiyar ƴan Legas Hoto: @jidesanwoolu
Asali: Twitter

“Lagas, Ina mai bayar da hakuri a kan abunda ya faru, ina ba matasanmu hakuri, dan Allah ku bayar da damar samun zama lafiya. Kowani rai na da amfani.”

KU KARATA KUMA: An tsaurara matakan tsaro a Kaduna yayinda zanga-zanga ke yaduwa

A cewarsa, a lokacin da gwamati ta saka dokar ta baci na sa’o’i 24 a jihar Lagas kuma matasan suka take umurnin, babu wani shugaba na zanga-zangar da za a yi wa magana.

Yayinda yake wanke kansa daga harin rundunar sojin, Sanwo-Olu ya bayyana gudanarwar sojin a Lekki a matsayin abun bakin ciki.

Ya yi alkawarin gabatar da lamarin a gaban manya sannan kuma cewa zai nemi agajin Shugaban kasa a matsayinsa na kwamandan rundunar tsaro ta kasa.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa sabanin yadda aka yi ta yayatawa, ba a rasa rai ba.

“Ba a rasa rai ko guda ba kamar yadda ake ta yayatawa a soshiyal midiya... Mun zagaya asibitoci da wuraren ajiye gawa.”

A baya mun ji cewa jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ya ce ba zai taba kasance da hannu a cikin kowani irin barna da ta’addanci ba.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Matasa sun kone gidan iyayen Gwamnan Legas, Sanwo-Olu

Tinubu na martani ne ga harin daren ranar Talata, 20 ga watan Oktoba, wanda aka gano jami’an tsaro suna bude wuta a kan masu zanga-zangar EndSARS a Lekki da ke Lagas.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel