EndSARS: NBA ta sha alwashin maka rundunar soji kotu kan kashe kashen Lekki

EndSARS: NBA ta sha alwashin maka rundunar soji kotu kan kashe kashen Lekki

- Kungiyar lauyoyin Nigeria (NBA) ta yi Allah wadai da harin da jami'an rundunar soji suka kaiwa masu zanga zanga a Lekki Toll Plaza, a daren ranar Talata

- Kungiyar ta kuma sha alwashin shigar da rundunar soji da sauran hukumomin tsaro kotu a madadin iyalan wadanda aka kashe da wadanda aka jikkata

- Sai dai, rundunar soji, a cikin sanarwar da ta fitar a shafinta na Twitter, ta karya zargin da ake yi na cewar jami'an ta ne suka kashe masu zanga zangar

Kungiyar lauyoyin Nigeria (NBA) ta magantu kan kashe masu zanga zangar @ENDSARS da jami'an rundunar soji suka yi a Lekki Toll Plaza, a daren Talata a jihar Legas.

Rayuka da dama sun salwanta a wannan dare, yayin da hotuna da bidiyoyin da ke yawo a kafofin sada zumunta ke nuna yadda mutane da dama suka jikkata, aka kai su asibitoci daban daban.

Masu zanga zangar na bukatar kawo karshen cin zarafin da 'yan sanda ke yiwa al'umma. Gwamnatin jihar ta sanar da dokar ta baci ta awanni 24 a fadin jihar.

KARANTA WANNAN: Sabuwar zanga zanga ta barke a Abuja: An kashe mutum daya, da yawa sun jikkata

EndSARS: NBA ta sha alwashin maka rundunar soji kotu kan kashe kashen Lekki
EndSARS: NBA ta sha alwashin maka rundunar soji kotu kan kashe kashen Lekki - @OlumideAkpata
Asali: Twitter

A yayin da gwamna Babajide Sanwo-Olu ya tabbatar da cewa mutane da dama sun jikka, ya gaza yin magana kan wadanda aka kashe a harin.

Rundunar soji a shafinta na Twitter ta karyata zargin da ake yi mata na harbe harbe da kuma kashe masu zanga zangar duk da cewa faifayen bidiyo ya tabbatar da hakan.

Shugaban kungiyar NBA, Olumide Akpata, a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, ya yi tur da kisan da jami'an tsaron suka yi akan masu zanga zangar.

Ya yi kira ga manyan shuwagabannin soji da su gaggauta gano sojojin da suka aikata wannan danyan aikin domin yanke masu hukunci kamar yadda shari'a ta tanadar.

"Kungiyar NBA za ta gaggauta daukar mataki na maka rundunar sojin kotu, da sauran hukumomin tsaro a madadin iyalan wadanda aka kashe da kuma jikkata su.

"Lallai wannan kokari ne na tauye 'yancin su na yin zanga zangar lumana da kuma 'yan cinsu na yin rayuwa."

A wani labarin, Sakamakon kai hare hare ga jami'an 'yan sanda, fararen hula da kuma kakaba dokar ta baci ta awanni 24 a jihar Legas, rundunar 'yan sandan Legas ta haramta zanga zanga a fadin jihar.

KARANTA WANNAN: DSS ta gayyaci wani babban malamin addinin Kirista kan rikicin Jos

Rundunar 'yan sanda ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata ta hannun jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Olumuyiwa Adejobi.

Rundunar 'yan sandan ta kuma tabbatar da cewa masu zanga zanga sun kona ofishin rundunar na Orile da misalin karfe 10 na safiyar ranar Talata.

Sanarwar ta ce "Jami'an mu sun samu manyan raunuka, inda har muke samun jita jitar cewa daya daga cikinsu ya mutu," kamar yadda jaridar This Day Live ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel