An tsaurara matakan tsaro a Kaduna yayinda zanga-zanga ke yaduwa

An tsaurara matakan tsaro a Kaduna yayinda zanga-zanga ke yaduwa

- An jibge matakan tsaro a garin Kaduna da gidan gwamnatin jihar

- Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da zanga-zanga ke bazuwa a fadin kasar

- Ko a ranar Talata, 20 ga watan Oktoba, sai da masu zanga-zangar suka bukaci ganin Gwamna Nasir El-Rufai a gidan gwamnati

An tsaurara matakan tsaro a kewayen birnin Kaduna da gidan gwamnati a ranar Talata, 20 ga watan Oktoba yayinda zanga-zangar #SecureNorth ke kara yaduwa a fadin kasar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Rahoton jaridar ya bayyana an gano motocin yan sanda jibge a kewaye da shataletalen gidan gwamnati tare da yan sanda masu kayan aiki da misalin karfe 10:00 na safe.

KU KARANTA KUMA: EndSARS: Kada ka yi amfani da karfin iko kan masu zanga-zanga - Atiku ga Buhari

An tsaurara matakan tsaro a Kaduna yayinda zanga-zanga ke yaduwa
An tsaurara matakan tsaro a Kaduna yayinda zanga-zanga ke yaduwa Hoto: @GuardianNigeria
Asali: UGC

Masu zanga-zangar sun je gidan gwamnati a ranar Litinin inda suka ce lallai sai sun ga Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai.

A ranar Talata masu zanga-zanngar sun taru a majalisar dokokin jihar da misalin karfe 12:00 na rana tare da ganga da kayen kida suna rawa da ihun “A tsare arewa yanzu”, “A kawo karshen ta’addanci,”da kuma “A kawo karshen garkuwa da mutane.”

KU KARANTA KUMA: An yi arangama tsakanin ƴan sanda ta ɓata gari a Lagos, mutane 2 sun mutu

A wani labarin, Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya yi maza ya kai ziyara ga wadanda aka buda wa wuta wajen zanga-zangar #EndSARS a Lekki.

Mista Babajide Sanwo-Olu ya yi magana a dandalin Twitter da kimanin karfe 4:00 na safe.

Gwamnan ya kira lamarin abin takaici da bakinciki, ya ce abin ya da auku ya fi karfin ikon gwamnati, ya yi alkawarin yin jawabi a yau da safe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel