An kama mutane hudu da ake zargi da kai wa kwamandan yan sanda hari

An kama mutane hudu da ake zargi da kai wa kwamandan yan sanda hari

- Rundunar yan sandan jihar Ebonyi ta tabbatar da kamun mutane hudu da ake zargi da kai wa kwamandan yan sanda hari

- Bata garin dai sun far ma CSP Chinedu Onuoha da hari har sai da ya rasa inda kansa ya ke

- A yanzu haka suna nan tsare a hannun yan sandan

Rahotanni sun kawo cewa an kama mutum hudu da ke da hannu a cikin harin da aka kai wa CSP Chinedu Onuoha a jihar Ebonyi.

CSP Onuola na aiki a matsayin mukaddashin kwamanda na yanki a karamar hukumar Ohaukwu da ke jihar.

Wadanda aka kama sune Alieze Uchenna, Agbo Chinonso, Onwe Okechukwu, da Onwe Onyedikachi kuma suna tsare a hannun yan sanda yanzu haka, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: An yi arangama tsakanin ƴan sanda ta ɓata gari a Lagos, mutane 2 sun mutu

An kama mutane hudu da ake zargi da kai wa kwamandan yan sanda hari
An kama mutane hudu da ake zargi da kai wa kwamandan yan sanda hari Hoto: Globe Afrique
Asali: UGC

Bata gari ne suka kai wa kwamandan yankin, wanda ya shiga wani yanayi bayan harin, farmaki.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa harin na zuwa ne bayan tattaunawar tsaro da aka yi hedkwatar karamar hukumar Ohaukwu.

DSP Loveth Odah, jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Ebonyi, ya tabbatar da kamun nasu a ranar Talata.

Rundunar yan sandan ta ce samu bindigun AK-47 da aka sace daga hannun yan ta’addan.

A gefe guda, IGP Mohammed Adamu, a ranar Talata, ya ce an kama mutane 12 da ake zargin da hannunsu a kai hari tare da kone wani ofishin 'yan sanda a Benin, jihar Edo.

A wani jawabi da kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, Mista Frank Mba, ya fitar, ya bayyana cewa an samu bindigu kirar AK47 guda biyar da aka sace daga ofishin da aka lalata.

KU KARANTA KUMA: Fursuna 1,993 sun tsere daga gidan yarin Benin sakamakon zanga-zanga

IGP Adamu ya bada umarnin gaggauta tura yan sandan kwantar da tarzoma don kula da rayuka da kuma kula da dukiyoyin gwamnati da na jama'a a fadin kasar nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel