An yi arangama tsakanin ƴan sanda ta ɓata gari a Lagos, mutane 2 sun mutu

An yi arangama tsakanin ƴan sanda ta ɓata gari a Lagos, mutane 2 sun mutu

- An rasa rayuka biyu yayin arangama a tsakanin yan sanda da bata gari a Lagas

- Lamarin ya afku ne bayan gwamnan jihar ya sanya dokar ta-baci a fadin jihar

- Miyagun sun yi amfani da damar zanga-zangar EndSARS ne wajen aiwatar da mugun nufinsu

Kimanin mutum biyu ake zaton sun mutu a wani arangama da aka yi tsakanin yan sandan Lagas da yan daba a yanki Mushin da ke jihar, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Rahoton ya kuma bayyana cewa wasu mutane sun jikkata sakamakon raunin da suka samu daga harbin bindiga a yayin hargitsin.

Rikicin ya wakana ne bayan gwamnan jihar Lagas ya sanar da sanya dokar ta-baci na sa’o’i 24 a jihar, wanda ya fara aiki daga karfe 4:00 na yammacin ranar Talata, 20 ga watan Oktoba.

An yi arangama tsakanin ƴan sanda ta ɓata gari a Lagos, mutane 2 sun mutu
An yi arangama tsakanin ƴan sanda ta ɓata gari a Lagos, mutane 2 sun mutu Hoto: @PremiumTimesng
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Jerin jihohi 5 da suka rufe makarantu sakamakon zanga-zangar EndSARS

Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ce wadanda ke muhimman ayyuka ne kadai aka dauke wa dokar.

“Cikin dimuwa na kalli yadda zanga-zangar #EndSARS da aka fara cikin lumana ya zama bala’i wanda ke barazana ga lafiyar al’ummanmu,” in ji gwamnan yayinda yake sanar da dokar kullen.

“An rasa rayuka yayinda miyagu da yan iska ke boyewa a karkashin inuwar zanga-zangar don aiwatar da annoba a kasarmu.”

Duk da sanarwar, sai da masu zanga-zanga suka tattaru a wuraren zanga-zangar mabanbanta.

A gefe guda, hukumar kula da gidajen gyaran hali na Najeriya (NCS) ta tabbatar da cewa fursuna 1,993 sun tsere daga gidan yarin da ma su zanga-zanga su ka balle ranar Litinin a Benin, jihar Edo.

Legit.ng Hausa ta rawaito yadda wasu batagarin matasa su ka balle wani gidan yari da ke kan titin Sapele a birnin Benin da safiyar ranar Litinin.

KU KARANTA KUMA: Anzo wajen: Zanga-zangar #EndSARS ta sauya zani, ta koma ta'addanci a Filato

Sakamakon hakan, gwamnatin jihar Edo ta sanar da saka dokar ta baci ta sa'a 24.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel