Buhari ya nada Aisha Dahir Umar a matsayin sabuwar DG ta PENCOMM

Buhari ya nada Aisha Dahir Umar a matsayin sabuwar DG ta PENCOMM

- Majalisar dattijai ta kada kuri'ar amincewa da nadin Aisha Dahir Umar a matsayin shugabar hukumar fansho ta kasa

- Shugaban marasa rinjaye a majalisar dattijai, Sanata Eyinnaya Abaribe, ya soki nadin Aisha

- Sanata Abaribe ya ce nadin Aisha ya sabawa kundin dokokin hukumar PENCOM da na tsarin daidaito a rabon mukaman tarayya

Majalisar dattijai ta tabbatar da nadin Aisha Dahir Umar a matsayin sabuwar shugaba (DG) hukumar fansho ta kasa (PENCOM).

A cikin watan Satumba ne shugaba Buhari ya bukaci majalisar dattijai ta amince da nadin Aisha a matsayin DG ta PENCOM.

Sai dai, bayan an karanta wasikar shugaba Buhari a zauren majalisa, Sanata Enyinnaya Abaribe, shugaban marasa rinjaye, ya ce nadin Aisha ya sabawa dokokin PENCOM da tsarin daidaito wajen rabon mukamai a tarayya.

Sanata Abaribe ya bayyana cewa sashe na 20(1) da na 21(2) na kundin hukumar PENCOM ya nuna cewa ba za a nada DG biyu a jere daga yanki guda ba.

KARANTA: Daya daga cikin matasan da ke jagorantar zanga-zanga ya janye hannunsa, ya bayyana dalilinsa

Dan majalisar na wadannan kalamai ne saboda tsohon shugaban PENCOM daga yankin arewa maso gabas ya fito kamar yadda ita ma sabuwar DG Aisha ta fito daga jihar Adamawa da ke yankin.

Aisha Dahir ta zama shugabar PENCOMM bayan Hanne Musawa ta gaza nuna shaidar NYSC
Aisha Dahir Umar
Asali: Twitter

Sai dai, shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmed Lawan, ya ce duk wani korafi dangane da nadin Aisha kamata ya yi a turawa kwamitin da ya tantance ma su son mukamin.

Lawan ya bayyana cewa jayayyar da Sanata Abaribe ke yi a kan nadin Aisha ba ta da tushe balle makama.

"An rushe tsohon shugabancin hukumar, rayuwar waccan shugabancin hukumar ta kare. Wannan sabon shugabanci ne bayan an rushe wancan," a cewar Lawan.

KARANTA: Duk don a bata gwamnatin Buhari ne - Sheikh Jingir ya bayyanan nufin ma su zanga-zanga

Duk da wani mamba a majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele, ya sake sukar nadin Aisha, hakan bai hana mambobin majalisar dattijan kada kuri'ar murya ta nuna amincewa da bukatar shugaba Buhari ba.

Sauran wadanda aka nada a matsayin kwamishinoni a hukumar PENCOM sun hada da Oyindasola Oni, Clement Oyedele Akintola, Ayim Nyere, da Charles Emukowhate.

Majalisar ta ki amincewa da nadin Hanna Hanney Musa Musawa a matsayin kwamishina saboda ta gaza nuna shaidar kammala bautar kasa da hukumar NYSC ke bayarwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng