Masoyan Shugaba Buhari sun cika hanya, su na zanga-zanga a Ribas

Masoyan Shugaba Buhari sun cika hanya, su na zanga-zanga a Ribas

- Wasu su na zanga-zangar goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari a jihar Ribas

- Masu zanga-zangar sun dauko tattaki ne tun daga Polo Club zuwa manyan hanyoyi

- Wadannan dakarun ba su adawa da masu kiran a gyara sha’anin aikin ‘yan sanda

Yayin da ake kokarin dakatar da zanga-zanga, wasu magoya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari sun fita su na irin ta su zanga-zangar.

Labari ya zo mana cewa an samu magoya bayan tafiyar Muhammadu Buhari da yanzu su ka cika gari su na tattaki a babban birnin jihar Ribas.

A daidai lokacin da masu fafutukar #EndSARS su ke ganiyar zanga-zanga, masu goyon bayan shugaban Najeriya sun cika garin Fatakwal makil.

KU KARANTA: IGP ya bada umarnin a baza Jami'ai da su yi maganin masu tada hatsaniya

Rahotanni sun ce masu wannan tattaki da zanga-zanga sun fito ne daga dukkanin kananan hukmomi 23 na Ribas, su ka hadu a yankin Polo Club.

Masu wannan zanga-zanga su na kiran a kawo karshen ta’adin da ‘yan sanda su ke yi a kasar nan, tare da kuma nuna goyon baya ga gwamnati mai-ci.

Kamar yadda hotuna da aikinsu ya nuna, jama’an sun jaddada mubaya’a ga Muhammadu Buhari.

Wadannan mutane su na dauke da tulin takardu da su ke cewa “We Say Yes To Victims Support Fund, da kuma “We Say Yes To President Buhari”

KU KARANTA: An sake kona ofishin 'Yan Sanda a Kudancin Najeriya

Masoyan Shugaba Buhari sun cika hanya-hanya, su na zanga-zanga a Ribas
Masoyan Shugaba Buhari Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Ma’ana dai su na goyon bayan a tallafawa wadanda su ka fada hannun danyen aikin ‘yan sanda, tare da kuma goyon bayan shugaban kasa Buhari.

Enefaa Georgewill, shugaban kungiyoyi masu zaman kansu a Ribas, ya bayyana cewa ba su san da zaman wannan masu zanga-zanga a ranar Talata ba.

Dazu kun ji yadda gwamnatin Legas ta yi asarar sama da N200m a dalilin zanga-zangar #EndSARS da aka kusan kwanaki goma da su ka wuce.

An saba biyan kudin amfani da hanyoyi a Legas, wannan ya kan taimaka wa tattalin jihar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng