Daya daga cikin matasan da ke jagorantar zanga-zanga ya janye hannunsa, ya bayyana dalilinsa

Daya daga cikin matasan da ke jagorantar zanga-zanga ya janye hannunsa, ya bayyana dalilinsa

- Rundunar 'yan sanda ta haramta duk wani nau'in tarurruka ko zanga zanga a fadin jihar Lagos daga ranar Talata 20 ga watan Oktoba

- Haka zalika, rundunar ta tabbatar da cewa, masu zanga zangar #EndSARS sun kona ofishin rundunar na Orile, jihar Lagos tare da jikkata jami'an ta

- Rundunar ta kuma ce ba za ta lamunci tashin hankula a jihar ba, ganin yadda aka samu gurbatattu a cikin masu zanga zangar

Ɗan-gwagwarmaya, Segun 'Sega' Awosanya (@Segalink), ya sanar da janye hannunsa daga zanga-zangar kawo ƙarshen sashe na musamman na yaƙi da fashi da makami(#EndSARS).

Ɗan gwagwarmaya ƴanchi, wanda ya jagoranci yaki da tozarci da muguntar ƴansanda a shekarar 2017 wanda kuma ya kasance jagaba a zangar-zangar kwanan nan, ya ce zanga-zangar ta sauya akala inda yace ma su wasu manufofi daban-daban sun ƙwace ragamar zanga-zangar.

DUBA WANNAN: Muhimmin sakon shugaba Buhari ga masu zanga zanga - Ministan Matasa

Ya wallafa a shafinsa na tuwita inda ya rubuta "dukkan wani yunƙuri na magana dasu ta hankali cikin sauki da masalaha ya tashi a banza. Na yarda cewa kowa yana da hankali sosai wajen fuskantar sakamakon tabarbarewar al'amura.''

Daya daga cikin matasan da ke jagorantar zanga-zanga ya janye hannunsa, ya bayyana dalilinsa
Segalink
Asali: Twitter

A cikin wata hira da aka yi da shi, ya ƙara da cewa; "duba ga yadda ake kai hari ga manyan mutane da kuma amfani da wannan dama don samar da kuɗi ta hanyar ƙungiya mai zaman kanta wadda bata da sahalewar hukuma.

DUBA WANNAN: Buhari ya aika muhimmin sako zuwa rundunar 'yan sanda a kan ma su zanga-zanga

"Hakan gaskiya ya zama barazana ga tsaron ƙasarmu da kuma yunkurin mayar da matasanmu ƴan tawaye da sunan zanga-zangar kawo ƙarshen sashe na musamman mai yaƙi da fashi da makami (#EndSARS). Shin wannan ba rashin hankali bane?"

Sakamakon kai hare hare ga jami'an 'yan sanda da fararen hula gwamnati ta kakaba dokar ta baci ta awanni 24 a jihar Legas, rundunar 'yan sandan Legas ta haramta zanga zanga a fadin jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel