Da dumi-dumi: An kona ofishin 'yan sanda a Legas

Da dumi-dumi: An kona ofishin 'yan sanda a Legas

- Wasu matasa da ake kyautata zaton 'yan daba ne sun kai hari sun kona ofishin 'yan sanda da ke Orile Iganmu a Legas

- Wasu ganau sun bayyana cewa lamarin ya faru ne misalin karfe 9.45 na safiyar ranar Talata 20 ga watan Oktoba

- Baya ga ofishin 'yan sanda na Orile Iganmu, an kuma sake kone wani ofishin 'yan sanda da ke Ifelodun a jihar ta Legas

Wasu da ake zargin 'yan daba ne sun kona ofishin 'yan sanda da ke Apapa Iganmu a jihar Legas kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne misalin karfe 9.45 na safiya a cewar wani da abin ya faru a idonsa.

Mai magana da yawun karamar hukumar Orile-Iganmu, Ayo Micheal ya ce, "Eh, an kai hari ofishin 'yan sandan.

DUBA WANNAN: A kan tattaro min takardun neman aiki a kalla 200 duk lokacin da na tafi ziyarar aiki - Pantami

Bata gari sun banka wa ofishin 'yan sanda wuta a Legas
Ofishin 'yan sanda a Legas. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: ENDSARS: Ku tanadi katin zabe, ku tabbatar kun kaɗa kuri'un ku - Fatima Ganduje

"Ofishin da aka kona yana Apapa Iganmu amma shi ke kula da yankunan Iganmu a Apapa Iganmu da garin Orile da ke Coker/Aguda."

Wasu sun ce harbin wani matashi cikin masu zanga-zanga da dan sanda mai aiki da ofishin na Orile ya yi ne ya janyo suka fusata su har ta kai sun kone ofishin 'yan sandan.

Babu wani jami'in dan sanda a cikin ofishin a lokacin da matasan suka banka wa ofishin wuta kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A wani labarin daban, wasu da ake zargin 'yan daba ne sun kona ofishin 'yan sanda da ke karamar hukumar Ifelodun na jihar Legas.

Wasu da lamarin ya faru a gabansu sun tabbatar wa The Punch afkuwar abin a ranar Talata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164