Rikicin APC na cikin gida: Marafa ya nufi kotun koli a kan taron jam'iyya

Rikicin APC na cikin gida: Marafa ya nufi kotun koli a kan taron jam'iyya

- Rabewar bangare biyu na Jam'iyyar APC ta jihar Zamfara na cigaba da barkewa wanda har hakan zai kai ga kotun koli dake Abuja

- Sakamakon taron Jam'iyyar APC da aka yi a ranar Litinin, 19 ga watan Oktoba, wanda aka nada shugabannin Jam'iyyar na jihar Zamfara ya jawo rikici

- Kamar yadda bangaren da Sanata Marafa ke jagoranta ke ganin cewa kotun daukaka kara ta yanke hukuncin da basu gamsu da shi ba, zasu kai kara kotun koli

Rikicin cikin jam'iyyar APC ta jihar Zamfara na cigaba da aukuwa tsakanin bangarorin guda biyu, wanda har kotu bata gama hukunci akai ba, Legit.ng ta wallafa.

Bangare daya na jam'iyyar, wanda Sanata Kabiru Marafa ke jagoranta sun ce za su daukaka kara zuwa kotun koli akan hukuncin da kotun daukaka kara ta Sokoto tayi akan taron jam'iyyar.

Kamar yadda kotun daukaka kara ta Sokoto ta tabbatar kuma ta gamsu da hukuncin da taron nadin shugabannin jam'iyyar da akayi a ranar Alhamis, 15 ga watan Oktoba, wadda Alhaji Lawal Liman ya jagoranta.

Kotun daukaka karar ta Sokoto ta yanke hukuncin da babbar Kotun Zamfara, wacce ta rushe duk nadin da taron yayi.

Bakyasuwa yace bangaren da Marafa ke jagoranta basu amince da hukuncin kotun daukaka karar ba. Yace don kawai tsohon Gwamna Abdulaziz Abubakar Yari na jagorantar dayan bangaren baya nufin sune za su nada shugabannin Jam'iyyar.

Ya kuma zargi shugabannin Jam'iyyar APC na kasa akan mara wa bangare daya baya, da nuna son kai wurin hukunci. Yace bangarensu na bukatar hukuncin gaskiya da gaskiya.

KU KARANTA: EndSARS: Jama'a sun fusata, yunwa ta yawaita a kasar nan - Gwamnoni

Rikicin APC na cikin gida: Marafa ya nufi kotun koli a kan taron jam'iyya
Rikicin APC na cikin gida: Marafa ya nufi kotun koli a kan taron jam'iyya. Hoto daga channelstv.com/guardian.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: Gwamnatin jihar Legas ta sake rufe makarantu

A wani labari na daban, daliban jami'o'i karkashin inuwar kungiyar daliban jami'o'i ta kasa ta ce hakurinsu ya kare sakamakon dogon yajin aikin da kungiyar malamai masu koyarwa na jami'o'i suka fada.

Daliban sun ce za su nuna rashin jin dadinsu a kan yadda yajin aikin ke tsawaita a ranar Talata. Sun ce za su fara zanga-zangar ne ta gaban katafaren ginin majalisar tarayya sannan su wuce zuwa ofishin ma'aikatar ilimi daga nan su garzarya zuwa ma'aikatar kwadago da aikin yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel