Yaro mai shekara 13 ya fado daga babbar mota ya mutu nan take yayin zanga-zanga

Yaro mai shekara 13 ya fado daga babbar mota ya mutu nan take yayin zanga-zanga

- Zanga-zangar nuna adawa da rundunar SARS ta kara daukan zafi tare da daukan sabon salo a ranar Litinin

- Wuraren taron ma su zanga-zanga sun kasance cibiyar taruwar jama'a; maza da mata, manya da yara

- Shugaba Buhari ya bukaci rundunar 'yan sanda ta bawa matasan da ke zanga-zanga tsaro

Wani yaro mai shekaru 13 da har yanzu ba a bayyana sunansa ba ya rasa ransa yayin zanga-zangar nuna da adawa da rundunar SARS a yankin Sapele na jihar Delta a ranar Litinin.

Jaridar Punch ta rawaito cewa yaron ya mutu ne sakamakon raunukan da ya samu bayan ya fado daga kololuwar babbar mota yayin da ta ke tafiya makare da ma su zanga-zangar ENDSARS.

Rahotanni sun bayyana cewa karar kwana ce ta kai matashin yaron ya shiga cikin samarin da ke zanga-zangar nuna adawa da zaluncin jami'an 'yan sanda da kuma kisan 'yan kasa ba bisa ka'ida ba.

DUBA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta fitar da jawabi a kan arangamar da ma su zanga-zanga suka yi da juna a Abuja

Yaro mai shekara 13 ya fado daga babbar mota ya mutu nan take yayin zanga-zanga
Yaro mai shekara 13 ya fado daga babbar mota ya mutu nan take yayin zanga-zanga
Asali: UGC

Wani shaidar gani da ido da ya nemi a boye sunansa ya bayyana cewa yaron ya daka tsalle daga kololuwar babbar mota domin ya fada kan wata babbar mota da ta zo gifatwa, amma sai ya yi rashin sa'a, ya fadi a kasa warwas.

"Kafin mu garzaya da shi zuwa asibiti ya ce ga garinku nan," a cewar majiyar jaridar Punch.

DUBA WANNAN: Duk don a rusa gwamnatin Buhari ne - Sheikh Jingir ya bayyana nufin ma su zanga-zanga

An lullube gawar matashin yaron da tufafi ma su launin tutar Nigeria tare da dora shi a kan babbar motar a yankin Amukpe da ke Sapele.

Da safiyar ranar Litinin ne Legit.ng Hausa ta wallafa labarin cewa dumbin mazauna wani gidan yari da ke birnin Benin a jihar Edo sun samu damar tserewa bayan wasu batagari da ake kyautata zaton 'yan daba ne sun balle gidan yarin.

Duk da babu cikakken rahoto daga kafafen yada labarai, sannan babu sanarwa daga hukumar kula da gidajen yari ta kasa, faifan bidiyon yadda batagarin su ka kai hari gidan yari ya shiga yanar gizo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng