Babbar magana: Ƴan majalisa suna shirin haramtawa kotu korar shugaban ƙasa da gwamnoni
- Dan majalisar wakilai mai wakiltar jihar Ribas ya mika wata gagarumar bukata a gaban majalisar
- Sabuwar dokar na son a sauya sashin kundin mulkin kasa wanda ya bada damar kwace kujerar shugaban kasa ko gwamna a kotu
- Bukatar na son haramta kwace kujerar dukkan masu takara inda daya daga cikinsu ke da nakasa a takardun karatu
Dokar da take sauraron kararrakin zabe wadda ke hana shugaban kasa da gwamnan da aka zaba, saboda gibin wani kwalin ilimi na abokan takaransu yana kan hanya a majalisar wakilai.
Dokar wannan al'amarin wacce jaridar Vanguard ta gani a ranar Litinin tana bayyana bukatar sauya kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, domin bai wa dan takarar shugaban kasa ko gwamna kariya wadanda abokan takararsu ke da matsala a takardun makaranta.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan sanda sun harba wa masu zanga-zanga barkonon tsohuwa a Abuja

Asali: Twitter
Bukatar ta bayyana a gaban majalisar ne ta hannun Solomon T. Bob dan Jam'iyyar PDP daga jihar Ribas.
Bukatar tana son a sauya sashi na 142 sakin layi na 1. Dokar ta ce matukar an zabi mutum a matsayin shugaban kasa, za a iya soke zabensa matukar akwai wata nakasa a takardun makarantun abokin takararsa da aka zabesu tare.
Sabuwar dokar tana son a sauya sashi na 142 na kundin tsarin mulkin inda za a iya kwace kujerar mataimakin kadai sannan a saka wani a maimakonsa.
KU KARANTA KUMA: Da ɗuminsa: Yan ta'adda sun kaiwa jami'an ƴan sandan RRS hari a Lagos
A gefe guda, Shugaban arewa a Kudu, Alhaji Musa Saidu, ya bukaci 'yan kabilar Ibo da su manta da batun shugabancin kasa a 2023 idan suka kasa tabbatar da zaman lafiya.
A wata tattaunawa da Saidu, ya ce masu yi wa 'yan Ibo alkawarin shugabancin kasa babu bukatar su cike gibin rashin zaman lafiya da ya mamayesu suna yaudararsu ne kawai.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng