NPF ta fitar da jawabi a kan arangamar da ma su zanga-zanga suka yi da juna a Abuja
- Zanga-zangar neman a rushe rundunar SARS ta fara sauya salo a sassan Najeriya da ta samu karbuwa
- Rahotannin baya bayan nan sun nuna cewa ana yawan samun kai hari a kan ma su zanga-zangar adawa da ma su zanga-zangar nuna goyon bayan rundunar SARS
- Kwamishinan 'yan sandan Abuja, Bala Chiroma, ya fitar da jawabi dangane da wata arangama da ma su zanga-zangar suka yi ranar Litinin
An samu barkewar rikici da hatsaniya da safiyar ranar Litinin bayan ma su zanga-zangar adawa da SARS da ma su goyon bayan SARS sun yi arangama a Abuja, kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.
Kwamishinan 'yan sandan Abuja, Bala Ciroma, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da sanar da cewa babu asarar rai.
A cikin sanarwar da ta fitar, kakakin rundunar 'yan sanda Abuja, ASP Mariam Yusuf, ta ce kwamishinan 'yan sanda ya bayyana cewa rikicin ya rincabe ne bayan ma su adawa da SARS sun yi arangama da ma su goyon bayan SARS.
KARANTA: Yadda na samo mana kwangilar tono gawa daga kabari a kan N2m - Abdullahi Dogo
Kazalika, rundunar 'yan sandan ta tabbatar da mutuwar Anthony Onome, wani mai zanga-zangar adawa da SARS, sakamakon raunukan da ya samu ranar Asabar bayan wasu batagari sun kaiwa ma su zanga-zanga hari a unguwar Kubwa.
"Kwamishinan 'yan sandan birnin tarayya (FCT), Bala Ciroma, ya yi kira ga ma su zanga-zanga su zauna lafiya da juna biyo bayan arangamar da ta faru tsakaninsu a kwaryar birnin Abuja da sanyin safiyar ranar Litinin, 19 ga watan Oktoba.
KARANTA: Duk don a rusa gwamnatin Buhari ne - Sheikh Jingir ya bayyanan nufin ma su zanga-zanga
''Rahoton sakamakon binciken farko-farko ya nuna cewa ba a samu asarar rai ba, amma an kone mita guda daya yayin arangamar. Duk da hakan, kwamishina ya bayar da umarnin gudanar da bincike a kan lamarin.
"A wani labarin, rundunar 'yan sanda ta yi Alla-wadai da kai hari a kan wani mai zanga-zangar adawa da SARS a yankin Kubwa ranar Asabar, 17 ga watan Oktoba, 2020.''
A wani labarin da Labarin mai nasaba da wannan da Legit.ng ta wallafa, sauyawar salon zanga-zangar ya jawo sakin sojoji zuwa kan titunan birnin Abuja.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng