ArewaMufarka: Aisha Buhari ta kaddamar da wasu sabbin bidiyo a kan yakar rashin tsaro

ArewaMufarka: Aisha Buhari ta kaddamar da wasu sabbin bidiyo a kan yakar rashin tsaro

- Uwargidan Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta kaddamar da kamfen akan halin da kasa ta ke a ranar Asabar a shafinta na Twitter

- Ta wallafa bidiyon wasu mutane 5 ne wadanda ke rike da takardu na neman taimakon gaggawa akan rashin tsaro dake Najeriya

- A cikin bidiyon, akwai waka mai taken aceci jama'a wadda hakan ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani

Uwargidan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, ta kaddamar da sabon kamfen akan rashin tsaron dake kasar nan a shafinta na Twitter.

Kamar yadda ta kaddamar da kamfen din nata mai take "Mu farka Arewa", an nuno wasu bidiyoyi guda 2, wadanda ke nuna mutane 5 da takardu da aka rubuta "A kawo karshen rashin tsaro cikin gaggawa; A daina ta'addanci; rayuwarmu tana da muhimmanci ".

Ta wallafa bidiyon ne da wata wakar Hausa, wadda har a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, wadda hakan ya jawo cece-kuce kala-kala.

Wadda wakar take nuna neman taimako na gaggawa wato Achechijamaa.

Mutane fiye da 396,000 sun duba bidiyon Achechijamaa kuma sun yaba da kokarin uwargidan shugaban kasar.

KU KARANTA: PDP ta lallasa APC, ta yi nasarar lashe zabukan kananan hukumomi a Bauchi

ArewaMufarka: Aisha Buhari ta kaddamar da wasu sabbin bidiyo a kan yakar rashin tsaro
ArewaMufarka: Aisha Buhari ta kaddamar da wasu sabbin bidiyo a kan yakar rashin tsaro. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: FG ta ja wa masu zanga-zangar EndSARS kunne da kakkausar murya

A wani labari na daban, daliban jami'o'i karkashin inuwar kungiyar daliban jami'o'i ta kasa ta ce hakurinsu ya kare sakamakon dogon yajin aikin da kungiyar malamai masu koyarwa na jami'o'i suka fada.

Daliban sun ce za su nuna rashin jin dadinsu a kan yadda yajin aikin ke tsawaita a ranar Talata.

Sun ce za su fara zanga-zangar ne ta gaban katafaren ginin majalisar tarayya sannan su wuce zuwa ofishin ma'aikatar ilimi daga nan su garzarya zuwa ma'aikatar kwadago da aikin yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel