Ba don masu zanga-zanga bane; DHQ ta yi karin haske a kan sabon atisayen 'murmushin kada'

Ba don masu zanga-zanga bane; DHQ ta yi karin haske a kan sabon atisayen 'murmushin kada'

- Rundunar soji ta za ta fara atisayen murmushin kada na shekarar 2020

- Atisayen wannan shekarar ya sha bamban da na sauran shekarun baya saboda zai waiwayi laifukan da ake aikata wa ta yanar gizo

- A cewar rundunar sojin, atisayen zai fara ne daga watan Oktoba zuwa watan Disamba 2020

Rundunar soji ta sanar da cewa sabon atisayen 'murmushin kada' da ta kaddamar bashi da wata nasaba da zanga-zangar da matasa ke yi a kan rushe rundunar SARS da zaluncin 'yan sanda.

A cikin wata sanarwa da hedikwatar tsaro ta fitar (DHQ), kanal Sagir Musa, kakakin rundunar soji ya ce kuskure ne a bayyana cewa an kaddamar da atisayen ne saboda zanga-zangar ENDSARS da ake yi a sassan kasa.

Kanal Sagir ya bayyana cewa rundunar soji ta nuna kwarewar aiki tun bayan barkewar zanga-zangar kusan sati biyu da su ka wuce.

KARANTA: Yadda na samo mana kwangilar tono gawa daga kabari a kan N2m - Abdullahi Dogo

"Hankalin rundunar soji ya kai ga wani rahoto da ke yawo a wasu kafafen sada zumunta tun bayan kaddamar da sabon atisayen 'murmushin kada VI' wanda za a fara daga ranar 20 ga watan Oktoba har zuwa ranar 31 ga watan Disamba, 2020.

Ba don masu zanga-zanga bane; DHQ ta yi karin haske a kan sabon atisayen 'murmushin kada'
Dakarun rundunar soji
Asali: Twitter

"Rundunar soji na son sanar da jama'a cewa akwai kuskure a cikin labarin da ake yadawa, atisayen 'murmushin kada' bashi da alaka da kowacce zanga-zanga.

"Ya kamata jama'a su sani cewa atisayen 'murmushin kada' al'amari ne na shekara-shekara da ake kaddamar da shi daga watan Oktoba zuwa Disamba na kowacce shekara.

DUBA WANNAN: IGP ya lissafa siffofin sabbin jami'an SWAT da za a fara bawa horo ranar 19 ga wata

"Batun cewa an kaddamar da atisayen a wannan shekarar saboda zanga-zangar ENDSARS ba gaskiya bane.

"Wanna atisaye bashi da nasaba da zanga-zangar da ake yi a sassan kasa. Rundunar soji ta nuna kwarewar aiki tun bayan barkewar zanga-zanga.

"Manufar atisayen 'murmushin kada' shine domin tabbatar da tsaron Najeriya da dukkan 'yan kasa," a cewar sanarwar.

Legit.ng Hausa ta gano cewa atisayen na 2020 zai sha bamban da na sauran shekarun baya saboda zai waiwayi ta'addanci ta yanar gizo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel