Dakarun sojoji sun yi artabu da yan bindiga a Filato, sun kashe mutum daya

Dakarun sojoji sun yi artabu da yan bindiga a Filato, sun kashe mutum daya

- Rundunar Operation Safe Haven sun sha artabu da yan fashi da makami a hanyar Bokkos-Barkin Ladi da ke jihar Filato

- A yayin arangamar, dakarun sojin sun yi nasarar kashe dan ta'adda daya

- Sun kuma yi nasarar kwato makamai daga hannun miyagun

Hedkwatar tsaro ta bayyana cewa a ci gaba da aikin kakkaba da suke yi domin fitar da yan bindiga da sauran miyagu a kasar, rundunar Operation Safe Haven sun dakile wani harin ta’addanci a hanyar Bokkos-Barkin Ladi da ke jihar Filato sannan suka kashe mutum daya.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jagoran labarai na rundunar tsaro, Manjo Janar John Eneche ya gabatar wa manema labarai a Abuja.

Janar Eneche ya bayyana cewa a yayinda suke amsa wani kira da suka samu kan aikin yan bindiga a daren ranar Juma’a a hanyar, rundunar da aka tura Kuba sun garzaya wajen sannan suka yi artabu da yan bindigan.

KU KARANTA KUMA: Tunda gwamnati ta amsa kokenku lokaci ya yi da ya kamata a daina wannan zanga-zanga - Lawan ga matasa

Dakarun sojoji sun yi artabu da yan bindiga a Filato, sun kashe mutum daya
Dakarun sojoji sun yi artabu da yan bindiga a Filato, sun kashe mutum daya Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

A cewarsa, “a yayin artabun, rundunar sun sha karfin yan fashin inda suka kashe mutum daya yayinda sauran suka tsere da harbin bindiga.

“Kayayyakin da aka samo daga yan ta’addan sun hada da bindigar gargaiya, wayoyin tafi da gidanka guda biyu, harsashi hudu da wuka daya.”

Ya bayyana cewa a yanzu haka, dakaarun na sanya idanu a dukkanin yankin domin hana yan ta’adda sukuni.

KU KARANTA KUMA: Tsaron Arewa: Ali Nuhu ya sha caccaka a wajen 'yan Najeriya saboda rashin shiga zanga-zanga

Ya bayar da tabbaccin cewa rundunar sojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro a kokarin da suke na dawo da zaman lafiya da tsaro a kasar ba za su kyale dukkanin makiyan kasar ba.

A wani labari na daban, Ƴar gidan gwamnan Kano, Fatima Ganduje-Ajimobi ta magantu a kan zanga-zangar #ENDSARS da ake don nuna rashin amincewa da zaluncin 'yan sanda.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng