Duk don a bata gwamnatin Buhari ne - Sheikh Jingir ya bayyanan nufin ma su zanga-zanga

Duk don a bata gwamnatin Buhari ne - Sheikh Jingir ya bayyanan nufin ma su zanga-zanga

- Sheikh Jingir ya ce zanga-zangar kawo ƙarshen sashe na musamman mai yaƙi da fashi da makami(#EndSARS) shiri ne na ruguza mulkin Buhari

- Har yanzu matasa na cigaba da zanga-zanga a Abuja da sauran wasu jihohin kudu duk da an sanar da rushe SARS

- Shugabannin majalisa da fadar shugaban kasa sun bukaci matasan su dakatar da zanga-zanga, gwamnati ta karbi korafinsu

Babban Malami kuma shugaban Malamai na ƙungiyar Izala (JIBWIS), Sheik Sani Yahaya Jingir, ya yi iƙirarin cewa zanga-zangar kawo ƙarshen sashe na musamman mai yaƙi da fashi da makami (SARS) da ke gudana a halin yanzu ƙullallen shiri ne don ruguza mulkin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da arewacin ƙasar nan.

"Abune a buɗe, wannan zanga-zangar shirin wargaza gwamnatin Buhari da kuma rushe ɗaukacin arewacin ƙasar nan.

KARANTA: Na samo mana kwangilar tono gawa daga kabari a kan N2m - Abdullahi Dogo

''Na faɗi haka saboda masu zanga_zangar sun buƙaci a rushe sashe na musamman yaƙi da fashi da makami(SARS) kuma an biya musu buƙatarsu amma har yanzu sun cigaba da zanga-zangar har wasu na kiran shugaban ƙasa da yayi murabus.

''Wannan na nuni da cewa akwai wani mummunan abu a ɓoye a cikin tafiyar," a cewar Sheik Jingir.

Duk don a bata gwamnatin Buhari ne - Sheikh Jingir ya bayyanan nufin ma su zanga-zanga
Sheikh Jingir
Asali: Facebook

Malamin yayi wannan iƙirari lokacin da ya ke gabatar da huɗubar Sallar Juma'a a Masallacin Ƴantaya da ke Jos; babban birnin jihar Plateau.

Sanann ya cigaba da cewa; "ba ma goyon bayan wannan tafiya ta zanga-zangar kawo ƙarshen sashe na musamman mai yaƙi da fashi da makami saboda babu gaskiya acikinta. An saka siyasa a ciki.

KARANTA: Zan iya hijira na bar Amurka idan na fadi zabe - Donald Trump

''Muna kira ga mutane da su ƙauracewa wannan tafiyar.

''Abin da muke buƙata shine addu'a don cigaban ƙasar mu da kuma ganin ƙarshen rashin tsaro da ya addabi al-ummomi da dama.''

Sheikh Jingir ya ce tafiyar zata kawo koma baya ga ƙasa a halin da ake ciki na fama da matsalar tsaro a sassan ƙasar nan, musamman a arewa.

A karshe, ya yi kira ga Shugaba Buhari da ya gaggauta ɗaukar mataki don kafin abu ya zo ya gagara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel