FG ta ja wa masu zanga-zangar EndSARS kunne da kakkausar murya

FG ta ja wa masu zanga-zangar EndSARS kunne da kakkausar murya

- Gwamnatin tarayya ta ja kunnen masu zanga-zanga, inda tace ba za ta lamunce da hakan ba

- Ministan Labarai, Lai Mohammed ya sanar da hakan a ranar Asabar, 17 ga watan Oktoba

- Yace yanzu haka, zanga-zangar ta canja salo, 'yan ta'adda ne kawai suke cin karensu babu babbaka

Gwamnatin tarayya ta ja kunnen masu zanga-zangar dakatar da SARS. Ministan labarai, Lai Mohammed ya fadi hakan a ranar Asabar, 17 ga watan Oktoba.

Mohammed ya ce gwamnatin tarayya ba za ta lamunci tada zaune tsaye ba a kasar nan.

Bayan zanga-zangar lumana wadda matasa suka yi akan SARS, gwamnatin tarayya ta ja kunnen jama'a, inda tace sam ba za ta yarda da tayar da tarzoma ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda Gwamnatin tarayya ta nuna fushinta akan zanga-zangar.

A ranar Asabar ne aka nuno Mohammed a tashar talabijin na NTA da daddare, wanda ke nuna shirye-shiryen karshen mako, wato "Weekend File".

Ministan ya ja kunnen akan yunkurin kashe gwamnan Osun, Adegboyego lokacin da yake yi wa masu zanga-zanga bayani, inda wasu 'yan ta'adda suka kai masa hari.

Yace duk wanda ya san farkon fitina bai san karshenta ba.

Yace damokaradiyya ta amince da zanga-zangar lumana, shiyasa kwana 11 da suka wuce gwamnati ta fahimci masu zanga-zangar. Amma yanzu haka, zanga-zangar ta canja salo, inda 'yan ta'adda suka samu damar cin karensu babu babbaka.

KU KARANTA: Dan sandan da ya jagoranci kafa rundunar SARS ya yi nadama

FG ta aike wa masu zanga-zangar EndaSARS muhimmin sako
FG ta aike wa masu zanga-zangar EndaSARS muhimmin sako. Hoto daga @LaiMohammed
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyon El-Rufai ya durkusa a gaban Sarki Ahmad Bamalli ya janyo cece-kuce

A wani labari na daban, CNG tace zata fara zanga-zanga maras tsayawa daga ranar Alhamis mai zuwa, akan rashin tsaron da ke addabar arewacin Najeriya.

Kamar yadda kungiyar tace, za ta yi hakan ne don sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari irin halin da jihohin arewa 19 suke ciki.

CNG tace, gwamnonin arewa sun gaza akan bai wa rayuka da dukiyoyin 'yan arewa cikakken tsaro, don haka tura ta kai bango.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel