Bidiyon wani mai bayar da hannu a titi da masu zanga-zanga suka karrama saboda kwazonsa
- A kwanan nan ne aka karrama wani dan sanda mai bayar da hannu a titi a yayinda yake bakin aiki
- A cewar rahotanni, wasu masu zanga-zanga a Calabar sun taru domin karrama shi saboda kwazonsa
- A wani bidiyo da aka wallafa, an gano inda masu zanga-zangar suka daga mutumin sama sannan suka ta yi masa liki da kudi
Wasu masu zanga-zangar a kawo karshen SARS a garin Calabar, sun karrama wani dan sanda mai bayar da hannu a titi, sun nuna masa so da kauna tare da tallafa masa.
A wani bidiyo da shafin @mediagist ta wallafa a Instagram, an nuno yadda matasan suka karrama mutumin tare da taya shi murna a yayinda yake bakin aikinsa.
A bisa ga wallafar, an bayyana mutumin mai suna Igri Nna Nkanu, a matsayin jajirtacce kuma mai kwazo a kan aikinsa.
KU KARANTA KUMA: Lawan ya dauki nauyin aurar da marayu da marasa gata su 100 a Yobe
Taron wanda ya gudana a ranar Juma’a, 16 ga watan Oktoba, ya nuno yadda mutane suka taru a kanshi, sannan suka daga shi sama a kan kokarin da yake yi kan aikinsa.
A cikin bidiyon, an gano wasu masu zanga-zanga suna masa liki da kudi.
Wani mai amfani da Twitter @JC_Jokes ya wallafa bidiyon inda ya rubuta:
“Masu zanga-zanga sun karrama mai bayar da hannu a titi mafi kwazo a Calabar. A koda yaushe za ku ganshi yana aikinsa da murmushi a fuskarsa a hanyar Mary Slessor. Har tara masa kudi suka yi. Yan Najeriya sun kasance mutane masu karamci duk da halin da ake ciki!”
KU KARANTA KUMA: Ambaliya: Buhari ya aika da tallafi Kaduna, Kano, Kebbi da wasu jihohi 9
A wani labari na daban, wata yar Najeriya ta je shafin soshiyal midiya domin murnar nasarar da ta samu bayan ta yi tattaki daga Lagas zuwa Abuja a kan babur.
Matashiyar mai suna Fehintoluwa Okegbenle ta wallafa wasu hotunanta da na sauran mutane da suka yi tafiyar a shafinta na Twitter.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng