Zan iya hijira na bar Amurka idan na fadi zabe - Donald Trump
- A cikin watan Nuwamba ake sa ran sake gudanar da babban zabe a kasar Amurka
- Za a fafata a zaben a tsakanin shugaba Donald Trump da abokin hamayyarsa Sanata Joe Biden
- Tuni harkokin yakin neman zabe da sauran shirye-shirye su ka yi nisa a manya da kananan biranen kasar Amurka
Shugaba Donald Trump ya ce zai iya yin hijira ya bar kasar Amurka idan har bai samu damar sake lashe zabe mai zuwa ba.
Ranar 3 ga watan Nuwamba aka tsayar domin gudanar da zaben kujerar shugaban kasa a Amurka.
Za a fafata zaben a tsakanin shugaba Trump, dan takarar Republican, da abokin hamayyarsa na jam'iyyar Democrat, Sanata Joe Biden.
DUBA WANNAN: Kyawawan hotunan matasa 12 da suka hadu a wajen bautar kasa kuma suka yi aure
Da ya ke magana yayin taron gangamin yakin neman zabensa da aka yi ranar Juma'a a Georgia, Trump ya ce ba zai ji dadi ya sha kaye a hannun ''dan takara ma fi tabarbarewa a tarihin siyasar Amurka'.
"Ba wai wasa na ke yi ba, ba ku san wani abu ba, ina fuskantar matsin lamba duk da ina takara ne da lusarin dan siyasa,"a cewar Trump.
"Me kuke ganin zai faru ifan na fadi zabe? ya ya zan yi da sauran rayuwata? dole ba zan ji dadi ba idan ya kasance na sha kaye a hannun dan takara mafi tabarbarewa a tarihin siyasar Amurka.
DUBA WANNAN: Ethiopia ta yi murnar shiga sabuwar shekara 2013 a yayin da kasashen duniya ke hangen 2021
“Ban san dai menene zai biyo baya ba, amma ina jin sai dai na yi hijira na bar kasar," kamar yadda Trump ya bayyana.
A makon da ya gabata ne Legit.ng ta wallafa rahoton cewa Fafaroma Francis, jagoran mabiya addinin Kirista a duniya, ya ce shugaban kasar Amurka, "Donald Trump ba kirista bane."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng