Bidiyon jami'in dan sanda rike da bindiga yana nadin tabar wiwi ya bayyana
- Yayinda gwamnati ke alkawarin gyare-gyare a hukumar yan sanda, wani bidiyo ya bayyana
- An ga dan sanda wajen mai abinci yana nadin tabar wiwi cikin jama'a
- Mutanen da ke wajen na kallonsa basu iya ce masa komai ba
Wani fai-fain bidiyon jami'in dan sandan Najeriya ya bayyana a kafafen ra'ayi da sada zumunta inda aka gansa yana nadin tabar wiwi a bainar jama'a rike da bindigarsa.
Wannan bidiyon ya bayyana ne lokacin da matasan Najeriya ke zanga-zangan neman sauyi a hukumar yan sandan Najeriya saboda irin cin zarafin da suke yiwa yan Najeriya.
Masu sharhi kan lamuran yau da kullum sun bayyana cewa ire-iren wadannan yan sanda ke kashe matasa bayan sun bugu.
Kalli bidiyon:
A bangare guda, shugaban yan sandan Najeriya, Muhammad Adamu, ya gargadi dukkanin jami’an yan sanda a fadin kasar kan amfani da karfi ga masu gudanar da zanga-zangar lumana.
A cewar wata sanarwa daga kakakin rundunar yan sanda; DCP Frank Mba, Shugaban yan sandan ya bayyana cewa yan kasa na da yancin nuna ra’ayinsu, haduwa, da kuma yin tattaki wanda ya zama lallai a ce yan sanda sun kare su a koda yaushe.
KU KARANTA KUMA: Gwamnan Yobe ya yiwa mutumin da ya mayar da kudi N1.7m kyauta mai tsoka
Shugaban rundunar a ranar Alhamis, 15 ga watan Oktoba, ya roki masu zanga-zangar da su ci gaba da gudanar da zanga-zangarsu cikin lumana, gidan talbijin din Channels ta ruwaito.

Asali: UGC
DUBA NAN: Zulum ya raba wa iyalai 5,000 kayan abinci, ya ziyarci dakarun soji a Borno
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng