Kotu ta yi fatali da rokon Onnoghen na tursasa Gwamnati ta biya sa N130m

Kotu ta yi fatali da rokon Onnoghen na tursasa Gwamnati ta biya sa N130m

- Lauyan da ya kai karar Gwamnati da sunan Walter Onnoghen ya sha kashi

- N.S. Nwawka ya na karar NIS da Gwamnatin Tarayya a wata kotun tarayya

- Wannan Lauya ya na ikirarin an hana tsohon Alkalin Alkalan kudin sallama

Wata babban kotun tarayya da ke zama a garin Abuja, ta yi watsi da karar da Walter Onnoghen ya kai hukumar NIS da gwamnatin tarayya.

Tsohon Alkalin alkalai na kasa watau Walter Onnoghen, ya na zargin hukumar kula da shiga fice da gwamnatin Najeriya da ci masa zarafi.

A makon nan Alkali mai shari’a Taiwo Taiwo ya saurari wannan shari’a da tsohon alkalin ya shigar ta hannun wani lauya, Dr. N.S. Nwawka.

KU KARANTA: Walter Onnoghen ya bayyana a kotun CCT

Da ya ke zartar da hukunci a ranar 12 ga watan Oktoba, mai shari’a Taiwo Taiwo ya ce ya duba karar, bamma ai gamsu da kukan.N.S. Nwawka ba.

Alkalin ya ki ba lauyan da ke kare tsohon alkalin damar da ya nema na zuwa kotun daukaka kara.

Ya ce: “Ina tambayarsa ko shin tsohon alkalin alkalan ya fada masa ba zai iya tsayawa kansa ba ne, ko ma ya shirya fafatawa da wasu a kotu.”

“Rokon da mai shigar da kara ya kawo bai da wani karfi a yadda ya ke, don haka na yi fatali da shi.” Inji babban Alkali Taiwo a ranar Litinin.

KU KARANTA: Kotu ta bada umarnin a kamo Alkalin Alkalan Najeriya

Kotu ta yi fatali da rokon Onnoghen na tursasa Gwamnati ta biya sa N130m
Walter Onnoghen guardian.ng
Asali: UGC

“Idan wanda ya shigar da karar ya na da lokacin da zai kawo wannan shiririta, wannan kotu ba ta da lokacin da za ta batar.” Aka yi watsi da shari’ar.

Jaridar The Nation ta ce Nwawka ya tafi kotu tun a watan Junairu, ya shigar da wannan kara mai lamba FHC/ABJ/CS/16/2020 a madadin Onnoghen.

A shekarar bara ne shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da Walter Onnoghen daga aiki, ya nada Tanko Muhammad a matsayin mukaddashin CJN.

Daga baya NJC ta bukaci ayi wa Onnoghen ritayar dole, a karshe dai ya ajiye aiki da kansa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel