Tsintuwa ba sata: Wani Bawan Allah da ya ke cigiyar duk kudin da ya tsinta

Tsintuwa ba sata: Wani Bawan Allah da ya ke cigiyar duk kudin da ya tsinta

- Umaru Kiri wani Direba ne da ba ya taba dukiyar da ya tsinta a mota ko hanya

- Wannan Bawan Allah ya taba tsintar har N1.3m amma ya sa aka kai wa mai ita

- A dalilin gaskiyarsa ne wata kungiya mai zaman kanta ta karrama shi a Yobe

A lokacin da ake ganin cewa mutane sun daina yin tsintuwa, su kuma yi cigiya a Najeriya, wani Bawan Allah ya yi abin da kowa ne zai iya ba.

Jaridar Daily Trust ta kawo labarin wani Malam Kiri Umaru, wanda direban mota ne a garin Damatutu, jihar Yobe, da ya maida miliyoyin kudi.

Kiri Umaru ya maida Naira miliyan 1.7 da ya tsinta a mabanbamtan lokuta ga masu kudin.

Wannan mutumi ya shafe shekaru 40 ya na tuka fasinjoji da kayan jama’a a kauyuka da manyan garuruwa, abin da bai yi shi ne gaba da kudin jama’a.

KU KARANTA: Manoma 150, 000 za su amfana da shirin Gwamnati a Katsina

A duk lokacin da Kiri Umaru ya tsinci kudi a cikin motarsa ko a wani wuri, sai ya yi kokari ya maida su wanda ya yi sakaci ko gaggacin zubar da su.

Jaridar ta ce Umaru mai shekaru 60 a Duniya ya na da mata biyu da ‘ya ‘ya har 12 wanda duka sun dogara da shi ne kafin su iya sa abinci a bakinsu.

Kudin da wannan mutumi ya tsinta karshe su ne N1, 380, 000 na wani da aka kunshe a bakar leda. Umaru ya dauki wannan kudi ya kai wa ‘yan kamasho.

Umaru ya dauko mutane ne daga Gashua zuwa Dapchi. Ya ce: “Ina dosan Garin Alkali daga Bayamari, sai na ga bakar leda, sai na fara tunani a raina.”

KU KARANTA: Mutane irinsu Farfesa Zulum ake bukata a Najeriya - Dr. Gadon-Kaya

Tsintuwa ba sata: Wani Bawan Allah da ya ke cigiyar duk kudin da ya tsinta
Malam Umara Kiri Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

“Na tambayi fasinjoji izini, na tsaya, na dauki ledar na bude bayan na boye, sai na ga kudi ne makil, daga nan sai na boye ba tare da na fada masu ba.”

A haka wannan mutumi ya yi har aka maida wadannan kudi ga mai shi, aka kuma yi masa godiya.

A wasu lokutan ya tsinci N150,000, N50,000, kuma duk ya yi cigiya, Ya ce ba zai samu kwanciyar hankalin hawa hanya dauke da abin da ba na shi ba.

Wannan ne ya sa kungiyar Yobe Civil Society Organisations ta nemo wannan dattijo, ta ba shi lambar yabo na Jakadan gaskiya da wadatar zuciya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel