Manyan kasa su na yi wa Seyi Makinde ta’aziyyar rashin tsohuwarsa

Manyan kasa su na yi wa Seyi Makinde ta’aziyyar rashin tsohuwarsa

- Mahaifiyar su Gwamnan Jihar Oyo ta rasu a ranar Alhamis dinnan

- Abigail Makinde ta haura shekaru 80 a Duniya a lokacin da ta rasu

- Shugaban kasa da Atiku Abubakar sun yi masa ta’aziyya tun a jiya

Shugaba Muhammadu Buhari da wasu gwamnonin jihohi da sauran manyan kasa sun yi wa gwamna Seyi Makinde ta’aziyyar rashin da ya yi.

A ranar Alhamis, 15 ga watan Oktoba, 2020, shugaban kasa ya fitar da jawabi ta bakin mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, a garin Abuja.

Garba Shehu ya ce:

KU KARANTA: Gwamnan Borno ya rabawa mutane 5000 abinci

“Shugaban kasa ya na aika sakon ta’aziyyarsa ga abokan arziki da ‘yanuwan gwamna Makinde da iyalinsa na rashin mahafiyarsu, Abigail Makinde.”

“Shugaban kasa ya na aika ta’aziyyarsa da abokai, ‘yanuwa da na-kusa da tsohuwar da ake cigaba da yada shaidar soyayya da kaunar da aka yi mata musamman ga talakawa da marasa karfi.”

Shi ma gwamnan Ogun, Dapo Abiodun ya yi wa takwaransa ta’aziyya. Gwamnan ya yi jawabi ne ta bakin sakataren yada labaransa, Kunle Somorin.

“Ina ta’aziyya ga Seyi Makinde na rashin mahaifiyarsa. Rashin uwa ya na zuwa da zafi, kuma ina taya ka da ‘yanuwanka addu’ar Ubangiji ya ba ku hakuri.”

KU KARANTA: Duk Gwamnonin Jihohi a yau babu kamar Farfesa Zulum - Dr. Gadon-Kaya

Manyan kasa su na yi wa Seyi Makinde ta’aziyyar rashin tsohuwarsa
Gwamna Seyi Makinde Hoto: www.politicsnigeria.com
Asali: UGC

“Allah ya jikanta, ya sa ta huta.” Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya aika wannan ta’aziyya a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis.

Sauran wadanda su ka yi maza su ka aika da ta’aziyyarsu tun a ranar da abin ya faru sun hada da Rt. Hon. Adebo Ogundoyin da Bolaji Ayorinde (SAN).

Kun ji cewa mahaifiyar gwamnan jihar Oyo, Abigail Makinde, ta rasu ta na da shekaru 81 a Duniya.

Tsohuwar ta rasu ne a gidan da ke unguwar Ikoloba, garin Ibadan, Oyo. Sanarwar mutuwar ta fito ne ta bakin Jagun Olubadan Cif Muyiwa Makinde.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng