Dangote, Abdulsamad, da Abdulrazaq sun yi muhimmiyar ganawa da jagororin zanga-zanga

Dangote, Abdulsamad, da Abdulrazaq sun yi muhimmiyar ganawa da jagororin zanga-zanga

- Fusatattun matasa sun cigaba da gudanar da zanga-zanga duk da fitar da sanarwar cewa an amsa bukatarsu, an rushe rundunar SARS

- Manyan attajiran kasa da ma su rike da mukaman siyasa sun tattauna da matasan da ke jagorar zanga-zangar

- Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya yi tsokaci a kan yadda tattaunawar ta kasance

Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya bayyana abinda ya faru yayin hirar da ya gabatar a kafar sadarwa ta ZOOM da masu ruwa da tsaki tare da sauran jagororin al-umma dangane da zangar-zangar kawo ƙarshen rundunar ENDSARS.

Tun ranar Juma'a ake gudanar da zangar-zangar a kan rusasshen sashe na musamman na yaƙi da fashi makami (SARS) na rundunar ƴansandan Najeriya.

Gungun jama'a, yawancinsu matasa, sun fito cikin lumana inda suke gudanar da zanga-zanga a jihohin Lagos, Osun, Oyo, Kwara, Kogi, da birnin tarayyar Abuja da sauran jihohin Najeriya daban-daban.

A yayin da zangar-zangar ta ɗau zafi, an gudanar da wata tattaunawa ta musamman, don kamo bakin zaren, a kafar sadarwa ta ZOOM; manhajar tattaunawa ta bidiyo.

KARANTA: Hotuna: Buhari ya gana da GEJ, Bagudu, Badaru da Buni a Villa

Wanda suka halarci tattaunawar sun haɗa da babban attajirin nahiyar Afirka, Aliko Dangote, shugaban rukunin bankin UBA; Tony Elumelu, Gwamman babban bankin Najeriya; Godwin Emifiele, Gwamna Okowa na jihar Delta, Gwamnan Jihar Kwara, da sannannen mawaƙin gambarar zamani, Ayodeji Balogun wanda aka fi sani da Wizkid.

Dangote, Abdulsamad, da Abdulrazaq sun yi muhimmiyar ganawa da jagororin zanga-zanga
Dangote da Elumelu
Asali: Instagram

Sauran sun haɗar da mai fafutikar kare haƙƙin dan-adam, Aisha Yesufu, malamin jami'a mazaunin England, Dipo Awojide da kuma ɗan kasuwar kafafen sadarwa Debola Williams.

Tattaunawar tasu ta yamutsa hazo a shafukan sada zumaunta, inda wasu daga cikin mutanen ke sukar yadda wasu daga cikin wanda suka halarci taron suka nuna rashin amincewa da fafutukar.

KARANTA: Muhimman aiyuka 8 na sabuwar rundunar SWAT - NPF

Da take fayyace abun da ya faru yayin tattaunawar, Aisha yesufu ta ce 'yan kasuwar suna so ne a kawo karshen zanga zangar, sai dai matasan da suka halarci tattaunawar sun dage akan ra'ayinsu.

"Gamayyar 'yan kasuwa ma su yaki da COVID 19 sun tattauna ta manhanjar zoom a kan #SASMUSTEND kuma nayi mamakin son kai irin na waddanda ake ikirarin sune shugabannin kasuwanci.

''Na fada musu cikin fushi cewa, shugaban kasa da kuma rundunar yan sanda suke da matsala ba wai matasan da ba abin da suka mora ba face shugabanni masu son kai. Bawai masu zanga zangar ne masu laifin ba, shugaban kasa da rundunar yan sanda sune masu laifin," kamar yadda Aisha yesufu ta wallafa a shafinta na tuwita.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng