Wata sabuwa: Ƴan daba sun tarwatsa masu zanga zanga a Kano

Wata sabuwa: Ƴan daba sun tarwatsa masu zanga zanga a Kano

- Wasu da ake zaton yan daba ne sun far ma masu zanga-zanga a jihar Kano

- Yan daban sun tarwatsa matasan wadanda suka fito don nuna damuwarsu a kan rashin tsaro a yankin arewacin kasar a daidai titin Kabuga

- Sun kuma yi masu sace-sacen wayoyi inda hakan ya sa suka hakura da gangamin

Rahotanni da muke samu a yanzu, ya nuna cewa wasu yan daba dauke da makamai sun tarwatsa zanga-zangar da wasu matasa ke gudanarwa a jihar Kano.

Matasa a jihar dai sun fito domin yin gangami a kan matsalar tsaro da ake fama da ita a arewacin Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Tashin farashin masara, tumatur, dawa: Jihar Nigeria da ke fuskantar ƙarancin abinci

Wata sabuwa: Ƴan daba sun tarwatsa masu zanga zanga a Kano
Wata sabuwa: Ƴan daba sun tarwatsa masu zanga zanga a Kano Hoto: @bbchausa
Asali: Twitter

Sashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa yan daban sun far wa masu zanga-zangar ne daidai titin kabuga da ke birnin tare da kwace-kwacen wayoyi.

Hakan ya tursasa wa masu zanga-zangar hakura da ci gaba da tattakin nasu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamna El-rufa’i ya sanya ranar buɗe makarantu a Kaduna

A wani lamari makamancin haka, wasu batagari, da ake kyautata zaton 'yan daba ne, dauke da makamai sun kai hari a kan wasu matasa da ke zanga-zanga a kan zaluncin da 'yan sandan rundunar SARS ke yi a fadin Najeriya.

'Yan daban, wadanda ke dauke da adduna, sun kai wa masu zanga-zangar farmaki a daidai Berger, bayan kusan sa'a daya da fara zanga-zangar.

Batagarin matasan sun ci mutuncin masu zanga-zangar har da masu wucewa, inda suka lalata ababen hawa da dama da ke wurin.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan dabar sun lalata akalla motoci 5 nan take, sannan sun ji wa masu zanga-zanga da dama munanan raunuka.

Wani matashi daga cikin wadanda aka ragargajewa mota ya ci kuka sharaf-sharaf da hawaye saboda bakin ciki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel