Da duminsa: Shugaban INEC ya sanar da ranar zaben shugaban kasa na 2023

Da duminsa: Shugaban INEC ya sanar da ranar zaben shugaban kasa na 2023

- Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ya bada muhimmiyar sanarwa

- Ya bayyana cewa za a yi zaben shugaban kasa mai zuwa a ranar 18 ga watan Fabrairun 2023

- Ya yi fatan alheri inda ya sanar da 'yan majalisar wakilai cewa sauran kwanaki 855 kafin zaben

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, a ranar Alhamis ya bayyana ranar zaben shugaban kasa mai zuwa.

Ya bayyana cewa, za a yi zaben a ranar 18 ga watan Fabrairun 2023 idan akwai rai, lafiya da zaman lafiya kamar yadda the Nation ta wallafa.

A sakon fatan alherinsa a yayin rantsar da kwamitin wucin-gadi na musamman a kan sake duba kundin tsarin mulkun kasar nan, shugaban hukumar zaben ya sanar da 'yan majalisar wakilai cewa akwai kwanaki 855 da suka rage kafin zaben.

KU KARANTA: Gide, shugaban 'yan bindigar Zamfara ya bada sharadin ajiye makamansa

Da duminsa: Shugaban INEC ya sanar da ranar zaben shugaban kasa na 2023
Da duminsa: Shugaban INEC ya sanar da ranar zaben shugaban kasa na 2023. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyon El-Rufai ya durkusa a gaban Sarki Ahmad Bamalli ya janyo cece-kuce

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya na kokarin rage rashin aikin yi a Najeriya, inda ta bayar da adireshin yanar gizo da matasa zasu samu damar samun jari, don tallafawa masu kananan sana'o'i.

Hadimar shugaba Buhari, Laureta Onochie ta sanar da hakan a ranar Laraba, 14 ga watan Oktoba ta kafar sada zumuntar zamani.

Dama ministan matasa da bunkasa wasanni, Sunday Dare, ya sanar da amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari da bayar da naira biliyan 75 don tallafawa matasa.

Yace za'ayi aikinne na tsawon shekaru 3, a kowacce shekara za'ayi amfani da naira biliyan 25, kamar yadda shugaban kasar ya amince.

Onochie tace, "gwamnatin tarayya ta saki adireshin yanar gizo ta shirin NYIF don tallafawa sana'ar matasa masu shekaru 18 zuwa 35."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel