Tashin farashin masara, tumatur, dawa: Babbar jihar Nigeria da ke fuskantar ƙarancin abinci

Tashin farashin masara, tumatur, dawa: Babbar jihar Nigeria da ke fuskantar ƙarancin abinci

- Yan Najeriya da ke zama a Lagas na fuskantar karancin abinci inda hakan ya sa muhimman kayayyakin abinci yin tashin gauron zabi

- Kaji, tolotolo, tumatir, agushi da masara na daga cikin kayayyakin da suka tashi

- Babban buhun jar masara da ake siyarwa N17,667 ya koma N20,167 a yanzu

Farashin muhimman kayayyakin abinci ya yi tashin gauron zabi a fadin manyan kasuwanni a jihar Lagas sakamakon karanci da suka yi.

Nairametrics ta ruwaito cewa wasu daga cikin wadannan kayayyaki da farashinsu ya daga sakamakon karancinsu sun hada da kaji, zabi, tumatir, agushi da masara.

Kwalin daskararren talotalo da ake siyarwa kan N17,333 a watan Disamban 2020, a yanzu ya koma N18,333.

KU KARANTA KUMA: Kalli budurwar da ta tuka babur daga Lagas zuwa Abuja cikin sa’o’i 13 (hotuna)

Tashin farashin masara, tumatur, dawa: Jihar Nigeria da ke fuskantar ƙarancin abinci
Tashin farashin masara, tumatur, dawa: Jihar Nigeria da ke fuskantar ƙarancin abinci Hoto: SustyVibes
Asali: UGC

Saboda karanci da yayi, kwalin daskararrun kaji da ake siyarwa kan N14,000 makonni biyu da suka gabata, ya koma N14,500 a yanzu.

Buhun jar masara da ake siyarwa N17,667 a baya ya koma N20,167. Yayinda ake siyar da buhun farar masara N20,000 a yanzu sabanin N17,000 da yake a baya.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamna El-rufa’i ya sanya ranar buɗe makarantu a Kaduna

Ana siyar da babban buhun barkono kan N17,000 yayinda ake siyar da madaidaicin buhu kan N9,000.

Ana siyar da babban kwandon tumatir kan N17,000 sabanin N16,000 da yake a baya a kasuwar Mile-12.

A watan Satumba 2020, ana siyar da babban buhun agushi kan N38,000 , amma a yanzu ya koma N46,500.

A wani labarin kuma, mun kawo a baya cewa Mai girma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koka game da halin da al’umma su ka samu kansu a sakamakon tashin farashin kayan abinci.

Shugaban kasar ya yi magana a ranar Laraba, 2 ga watan Satumba, 2020, ta bakin Malam Garba Shehu, babban mai taimaka masa wajen harkokin yada labarai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel