Direbana ya gamu da ajalinsa a hannun ‘yan zanga-zangar #EndSARS - Keyamo

Direbana ya gamu da ajalinsa a hannun ‘yan zanga-zangar #EndSARS - Keyamo

- Masu zanga-zangar #EndSARS sun yi sanadiyyar mutuwar Yohanna Shankuk

- Yohanna Shankuk ya na cikin direbobin Ministan kwadago, Festus Keyamo ne

- Ministan ya bada labarin yadda wannan zanga-zangar ta sa ya rasa yaron na sa

Ministan gwamnatin tarayya, Festus Keyamo SAN, ya koka game da zanga-zangar #EndSARS da ake cigaba da yi a fadin jihohin kasar nan.

Festus Keyamo ya bayyana cewa a sanadiyyar zanga-zangar da wasu su ke ta yi da nufin rusa jami’an SARS ne ya rasa mai tuka masa mota.

Ministan ya bada labarin yadda direbansa ya mutu wajen zanga-zangar. Ya ce masu zanga-zanga su ka zama ajalin Yohanna Shankuk a Abuja.

KU KARANTA: Sojoji sun yi magana game da zanga-zangar #EndSARS

Karamin ministan kwadagon da samar da aikin yi, ya yi wannan bayani ne a shafinsa na Twitter.

A labarin da Ministan kwadagon ya bada, an ji cewa direban na sa ya na tafiya salin-alin, wata mota ta bi ta kanshi, a sanadiyyar wannan hadari ya cika.

“Ina mai takaicin sanar da ku cewa Direbana Mista Yohanna Shankuk, ya mutu jiya a garin Abuja, a sanadiyyar zanga-zangar nan.” Inji Keyamo.

Ministan ya kara da cewa: “Wata mota da ta hango dinbin masu zanga-zanga sun nufo shatale-talen Berger, sai ta saki hannunta, ta kauce-hanya.”

KU KARANTA: Tsohon Minista ya bayyana abin da zai jawowa PDP asara 2023

Direbana ya gamu da ajalinsa a hannun ‘yan zanga-zangar #EndSARS - Keyamo
Festus Keyamo Hoto: www.ripplesnigeria.com
Asali: UGC

Ya ce: “Daga nan ta auka masa a lokacin da ya ke tafiya a kafa, ya na kan hanyar zuwa ofishina.”

A baya, Keyamo SAN ya zargi masu wannan zanga-zanga da tsageranci, ya ce wasu miyagu sun shiga cikin tafiyar #EndSARS domin su haddasa fitina.

Idan za ku tuna, wannan shi ne ra'ayin kungiyar MURIC, inda ta gargadi masu zanga-zangar #EndSARS su bi a hankali da masu boyayyar manufa.

Shugaban MURIC ya ce dole jama'a su yi hattara, akwai lauje a nadi a tafiyar #EndSARS.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel